'Yan ta'adda sun kona ofishin likitocin agaji a Burkina Faso
July 20, 2024Kungiyar likitocin bayar da agaji ta Doctors Without Borders ko kuma Medicens Sans Frontieres, ta sanar da cewa an kai wa ofishinta hari tare da kona shi, a garin Djibo na arewacin kasar Burkina Faso.
karin bayani:Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya
Kungiyar ta ce a cikin daren Larabar da ta gabata aka fara kai wa ofishin na ta hari da harbe-haren bindiga, a yankin da masu ikirarin jihadi suka mamaye tsawon shekaru biyu kenan yanzu, wanda ke kusa da iyaka da kasashen Nijar da Mali.
Karin bayani:MDD na fargabar fantsamar rikicin kasashen Sahel zuwa makwabta
Tun a cikin watan Satumbar shekarar 2022 ne kyaftin Ibrahim Traore ya kwace ikon mulkin kasar, wadda ke fama da hare-haren 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi na tsawon shekaru 10, inda ya yi alkawarin mayar da kasar kan turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma har yanzu bata sake zani ba.