Chadi: 'Yan tawaye za su koma teburin sulhu
July 23, 2022Talla
'Yan tawayen Chadi sun ce za su sake shiga tattaunawar sulhu da gwamnatin rikon kwaryar kasar bayan ficewar da suka yi daga tattaunawar a makon da ya gabata.
Matakin da suka sanar a ranar Jumma'a ya kara kyautata fatan shigarsu cikin tattaunawar kasa da aka shirya gudanarwa a watan gobe na Agusta a kasar ta Chadi. Tattaunawar ce ake sa ran za ta share fagen wareware rigingimun kasar kafin gudanar da zabe bayan da shugaban rikon kasar Mahamat Idriss Deby ya kwace iko da kasar jim kadan bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar da ta gabata.