1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yar kasar Senegal ta samu babban mukami a FIFA

Salissou BoukariMay 13, 2016

A karo na farko an zabi mace kuma 'yar kasar Senegal mai suna Fatma Samba Diouf Samoura a matsayin sakatare janar ta hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

https://p.dw.com/p/1IngB
Fatma Samoura
Fatma SamouraHoto: Getty Images/AFP/S. de Sakutin

Wannan dai shi ne karo na farko da wata mace ta samu wannan mukami a cikin babbar hukumar kwallon kafar ta duniya. Mai shekaru 52 a duniya, Fatma Samoura na matsayin wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin raya kasashe a Tarayyar Najeriya, inda take aiki tsahon shekaru 21 a karkashin Majalisar Dinkin Duniya musamman ma a fannin kula da agaji.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino, ya ce Fatma mace ce da ta taka rawar gani a fannoni da dama, kuma ta na da sanin harkokin kasa da kasa kasancewar ta yi ayyuka kan batutuwa masu wahalar gaske, inda ta nuna tana iya gina tare da jagorancin jama'a, kana mace ce da ke yin aiki da gaskiya wanda ke zaman ginshikin ci-gaban duk wani tsari.