Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici
October 10, 2024Hukumar lafiya ta Lebanon ta tabbatar da cewar daga cikin mutane kimanin dubu uku da hare-haren Isra'ila suka halaka a kasar har da yara kanana 1189. Ita ma Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta ce hare haren wata guda na jiragen yakin Isra'ila kan Lebanon sun raba aƙalla mutune miliyan 1.2 da muhallansu, almarin da ya sa dubban yara kwana a kan tituna.
Karin bayani:Sabbin hare-haren Isra'ila sun sa 'yan Lebanon tserewa
Sai dai kakakin asusun na Unicef a Lebanon Tess Ingram ya ce wajibi ne a gagauta samar wa yaran da ke watangaririrya a kan titiunan kasar musamman a birnin Beirut da matsuguni mai mutunci. Ya ce: "Yara kanana 'yan Lebanon suna bukatar kwanciyar hankali da zaman lafiya, ba sake jefa su cikin tarzoma ba. Barin su suna watangaririya kan tituna bayan raba su da matsugunansu, keta huruminsu ne. Masu ruwa da tsaki kan ayyukan agaji na MDD su gaggauta samar musu da sansanin da za su rayu cikinsa, su yi barci cikin mutunci, a maimakon barinsu suna kwana kan titunan a birnin Beirut."
Karin bayani:Rikicin Israila da Hezbollah: Mene ne sirrin kemewar Iran
Ummu-Rahma da 'y'ayanta shida ne ke kwance a titunan Beirut, kuma ta ce rikici ne ya tilasta musu kwana a kusa da bola. Tana fatan a kawo karshen yaki ko da ba za su samu damar komawa gidansu da aka yi raga-raga da shi ba. Ummu-Rahma ta ce: “Mun tsere daga gidanjanmu ba shiri, ba mu san yadda za mu fita ba. Mun ma taki sa'a, don mintuna biyar bayan ficewarmu ne hare-haren Isra'ila suka yi raga-raga da su. Da fari mun doshi sansanin 'yan gudun hijrara da aka ce mana an tanada, amma da muka isa sai muka tarar da shi ya cika makil ba masaar tsinke.”
Karin bayani:Hezbollah ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah
Kungiyoyin agaji na ci gaba da gina sansanoni don tarbar 'yan gudun hijira. Sai dai kamar yadda shugaban hukumar agaji ta Yasmeen da ke kasar Oman, Hasan Zahir ke cewa, muddin Isra,ila ba ta sassauta hare-haren da take kaiwa saman Beirut bisa zargin Iran da fasa kwabrin makamai ba, dole ne za a ci gaba da samun tasgaro a ayyukan agaji da gina sabin sansanonin.
Karin bayani:Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah
A nasa bangaren, firaiministan Isra'ila ya mai da martini kan sukar da kungiyoyin agaji ke masa na kai hare hare kan unguwannin da ke dankare da fararen hula, ba tare da bayar da isasshen lokacin tserewa ba, inda Benjamin Netanyahu ya ce: "Hanya mafificiya ga 'ya'yanku kanana da garuruwanku sh ine, ku yi wa kungiyar Hezbollah tawaye, ku ba mu bayanan sirri don gaggauta kawo karshen jagororinta da rumbunan makamanta. Yin haka ne kawai zai hana ku fuskantar irin makomar Gaza.”