Cinikayya mara shinge a kasashen Afrika
March 24, 2018Taron koli na musamman da shugabannin kasashen Afirka suka gudanar a Ruwanda ya dora matakin kirkiro da ciniki mara shinge a Afirka da walwalar tafiye tafiye ba da tarnaki ba kan hanya.
Wakilan gwamnatoci 44 na kasashen Afirka ciki har da shugabannin kasashe suka sanya hannu kan yarjejeniyar wadda a turancin Ingilishi ake kira "African Continental Free Trade Agreement" wato yarjejeniyar ciniki maras shinge a nahiyar Afirka.
Wannan dai tamkar mafarkin kasashen na Afirka ne ya tabbata inji jaridar ta Die Tageszeitung wadda ta kara da cewa rashin halartar taron daga bangaren Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka ya rage wa taron armashi.
Shi ma shugaban Yuganda Yuweri Museveni bai halarci taron ba. Kasashen biyu dai na nuna damuwa cewa masana'antunsu ba su da isashen karfin yin gogayya a yanzu.
Sauyin yanayi na tilasta yin kaura, abin da kuma ya shafi mutane miliyan 140 a duniya baki daya inji jaridar Neues Deutschland ta na mai ruwaito wani rahoton Bankin Duniya.
Jaridar ta ce sakamakon wani nazari da Bankin Duniya ya yi ya gano cewa a cikin shekaru gommai masu zuwa miliyoyin mutane ne sauyin yanayi zai tilasta musu yin kaura, matukar shugabannin siyasa ba su dauki kwakkwaran matakin magance tushen sauyin yanayin ba.
Jaridar ta ce sabon rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa a kasashen Afirka kudu da Hamadar Sahara mutane fiye da miliyan 80 za su kaura daga yankunansu na asali kafin nan da shekara ta 2050.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon ta leka kasar Afirka ta Kudu a kan batun dokar mallakar fili ta na mai cewa sabbin shirye-shirye kan dokar mallakar filaye sun janyo fargaba.
Ta ce gwamnatin Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan ba sani ba sabo kan manoma farar fata idan bukatar yin haka ta taso. Fiye da shekaru 20 bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata mahawara kan kwace filaye daga hannun farar fata a mika wa bakar fata ta sake kunno kai a Afirka ta Kudu. Ko da yake Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi kokarin kwantar da hankalin jama'a da cewa babu dalilin wata fargaba.