Yawaitar matasa da ke rungumar akidar IS a kasashen Turai
September 13, 2024Rahotanni sun nunar da cewa, masu tsattsauran ra'ayin adiinin Islama ne suka rudi matashi dan Ostiriya da 'yan sandan Jamus suka bindige har lahira bayan harin da ya kai musu da bindiga a birnin Munich. Sai dai matashin Emrah I. mai shekaru 18 a duniya da ya fito daga wani dan karamin kauye na Salzburg, ba ya wani zuwa Masallacin kauyensu, kana bai ajiye gemu ba balle kuma sanya jallabiya. Halayensa sun fara bayyana ne a farkon shekara ta 2023, lokacin da 'yan sandan Ostiriya suka gudanar da bincike sakamakon fada da ya yi a makaranta, inda aka samu bidiyo wasan "computer" da ya yi da kuma cikin wayarsa da tutar kungiyar al-Qaeda. Amma baya ga haka, babu abin da aka samu.
Yadda IS ke rudin matasa a Turai
'Yan sandan sun yi imanin cewa, matashin ya rungumi matsanancin ra'ayi ta hanyar Internet. Tun daga watan Janairun 2024 ne, kungiyar IS ta Khorasan IS-K ke karfafa gwiwar magoya bayanta su kai hare-haren kashin kai a wuraren tarurruka kamar wadanda ake gudanar da wasannin Olympics da na kwallon kafa a nahiyar Turai. Kwararru na ganin IS-K na tura wadannan sakonnin ne ga matasan da ke zaune a Turai.
Karin bayani: Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka
Lucas Webber mai bincike a cibiyar Soufan da ke birnin New York na Amurka, ya ce ana wanke wa yaran kwakwalwa ne ta hanyar Internet, inda ya ce: "Ina ganin tsawaita amfanin da shafin Intanet na taimakawa gaya wajen haduwa da wadannan mutane masu tsattsauran ra'ayi, inda suke amfani da wannan dama wajen cusa akidunsu ta hanyar amfani da kafar Intanet."
Kasashen da ta'addanci ya fi shafa a Turai
A makonnin baya-bayan nan, an cafke wani yaro dan shekaru 14 a duniya a Uruguay bayan da ya ayyana kansa a matsayin dan ta'adda mai zaman kansa. Haka ma a Switzerland, an cafke wani yaro dan shekaru 11 da haihuwa da ke yada sakonnin tsattsauran ra'ayi a kafafen sada zumunta na zamani. A cewar masani Pieter Van Ostaeyen da ya jima yana bincike a kan ayyukan kungiyar IS tare da kuma ke lura da shirin yaki da tsattsauran ra'ayi, yana kyautata zaton cewar akwai wasu manyan bangarori da ke wanke kwakwalen wadannan matasa.
Karin bayaMayakan jihadi na sake dabarun kai harini:
Shi ma daraktan da ke kula da nahiyar Afirka da Gabas ta Tsakiya da Kuma Asiya a cibiyar tuntuba da ke birnin London Moustafa Ayad ya ce: "Ya fi zama tamkar wani zaure da matasa ke sha'aninsu a kafar Internet da cikin al'umma, wadanda kuma ke son yin tasiri a wajen da suka samu kansu. In ka lura abin da matasan ke yadawa da harsunan da suke magana da su, na kama da na masu tsattsauran ra'ayi. Koyi da kungiyar IS, ya zamo jiki ga wadannan matasa."
Yawan shari'u kan ta'addancin IS a Turai
Tsakanin watan Maris na shekara ta 2023 da watan Maris na shekara ta 2024, masu bincike a wata cibiyar kula da yankin Gabas ta Tsakiya da ke birnin Washington na Amurka sun gano shari'u 470 da suke da nasaba da matsanacin ra'ayin kungiyar IS. Matasa da yara kimanin 30 ne aka gano, kamar yadda rahoton ya nunar. Akwai yuwuwar alkaluman sun haura haka, saboda da kasashe da dama ba sa sakin bayanai kan shekarun mutanen da aka kama.