1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: 'Yan ta'adda na sake dabaru

June 28, 2021

Sa'o'i 72 bayan kai wani mummunan harin ta'addanci kan rundunar sojojin Jamus da ke aikin wanzar da zaman lafiya a arewacin Mali, al'umma na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan sababbin dabarun maharan na kai hari.

https://p.dw.com/p/3vhOC
Symbolbild Drohne Bundeswehr
Sojojin Jamus sun fuskanci harin ta'addanci a Mali, bayan janye sojojin FaransaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A baya-bayan nan dai, mayakan jihadin na zafafa kai munanan hare-hare a kan rundunonin kasa da kasa masu hankoron tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar. Akalla sojojin Jamus 12 ne dai harin na yankin arewacin Mali ya jikkata, ciki har da wasu uku da suka ji mummunan rauni a tsakiyar makon jiya. Yehia Ag Mohamed wani kwararren mai bincike ne kana mamba a kawancen Convergence pour le développement du Mali, kuma a cewarsa kungiyoyin sun dauki dogon lokaci suna tsara aika-aikar. 

Karin Bayani: Jamus za ta ci gaba da horas da sojin Mali

An kai harin farko ne dai a garin Gossi da ke yankin Tombouctou ga sojojin rundunar Barkhane, a yayin da hari na biyu kan sojojin Jamus ya gudana a Tarkint  da ke yankin Gao na arewacin Malin. An dai kai harin ne, a daidai lokacin da ayarin motocin sojojin na Jamus ke rakiyar takwarorinsu na Mali da ke kan hanyarsu ta zuwa yankin Kidal. Rundunar sojojin ta Jamus dai, ta kwashe daukacin sojojinta da suka ji rauni domin mayar da su gida Jamus. #b#

Verletzte Soldaten aus Mali landen in Stuttgart
Jamus ta mayar da sojojinta da suka jikkata a Mali zuwa gida, don kula da lafiyarsuHoto: Christoph Schmidt/dpa/picture alliance

Sai dai a cewar Lamine Savané wani malami a jami'ar Segou, mayakan jihadin na cikin wani yanayi ne da ke nuni da cewa ba su da zabi. Wannan harin da ya rutsa da dakarun tsaron Jamus dai, ya kara zafafa mahawar a kasar kan hadarin da ke tattare da ci gaba da kasancewar sojojin a wasu kasashe musamman ma Mali da ke yankin Sahel, inda galibin jaridu suka kwatanta wannan matsalar da irin ababen da ke faruwa a kasar Afghanistan.  

Karin Bayani: Sharhi kan Neman aminta da juna a yankin Sahel

Wannan lamrin dai na zuwa a yayin da hankulan wasu 'yan kasar suka karkata kan ficewar sojojin kasa da kasa musamman na Faransa a kasar Malin. Jamus na daga cikin kasashen Yamma da sojojinsu ke hororar da dubarun yaki ga sojojin Mali, tare da bayar da daukin gaggawa ga rundunar MUNUSMA ta Majalisar Dinkin Duniya mai aikin wanzar da zaman lafiya da ke da dubban sojojin wanzar da zaman lafiya a kasar.