1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan cinikin man Najeriya ya ragu

July 7, 2023

Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu da kashi 28%, tun bayan da shugaban kasar Bola Tinubu ya janye tallafin man a karshen watan Mayu.

https://p.dw.com/p/4TYBM
Gidan sayar da man fetir a Abuja
Gidan sayar da man fetir na NNPC a Abuja Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Cikin watan da ya gabata, man fetir din da aka sayar a Najeriya na matsayin lita miliyan 48 ne da dubu 430, maimakon lita miliyan 66 da dubu 900 da aka saba kafin janye tallafin.

Man na fetir dai ya yi tsada a kasar sabanin yanda yake a gomman shekarun da suka gabata, a kasa mafi karfin arziki a nahiyar Afirka.

Rahotanni ma daga kasashen Kamaru da Benin da Togo, na nuna cewa 'yan kasuwanni bumburutunman fetir sun durkushe tun bayan da aka janye tallafin saboda tsadar makamashin a yanzu.

Dala biliyan 10 ne Najeriyar ta kashe a bara wajen biyan kudin tallafin man.

Bankin duniya kuwa a gefe guda ya ce Najeriyar na iya adana akalla biliyan biyar da miliyan 100  na dala daga janye tallafin da ma sauye-sauyen da Tinubu ya kawo a fannin hada-hadar kudaden ketare.