1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na yunkurin ganin an kawo karshen yakin Gaza

September 6, 2024

A ci gaba da rangadin da take yi a kasashen Gabas ta Tsakiya, Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta gana da takwaranta na Jordan Ayman Safadi, a birnin Amman domin tattaunawa kan kawo karshen yakin Gaza.

https://p.dw.com/p/4kMr1
Hoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

 Jamus ta sake rubanyawa kan kokarin da take yi na kawo karshen yakin Gaza ta hanyar yunkurin tattaunawar diflomasiyya da ministar harkokin wajen kasar Annalena Baerbock ke yi a kasashen Isra'ila da Jordan, inda za ta karkare da Saudiyya. Ministar ta sanar da takwaranta na Jordan cewa yakin da ya ki ci ya ki cinyewa ka iya zama babbar barazana ga zaman lafiyar kasashen Gabas ta Tsakiya da batun addini har ma da batun ruruta kyamar Yahudawa a fadin duniya.

Annalena Baerbock tare da ministan harkokin wajen Isra'ila
Annalena Baerbock tare da ministan harkokin wajen Isra'ilaHoto: GIL COHEN-MAGEN/AFP

"A wannan shiyya, da kuma ko'ina a fadin duniya samar da kasashe biyu masu cikakken iko na da matukar mahimmanci. To amma abin takaicin shi ne yadda Gabas ta Tsakiya ke rikidewa zuwa makwantar rikici. Godiya ga kasashen duniya musamman wadanda ke fadi tashin dakile bazuwar wannan tashin hankali a sauran kasashen yankin.”

Annalena Baerbock tare Faisal bin Farhan bin Abdullah ministan harkokin waje na Saudiyya
Annalena Baerbock tare Faisal bin Farhan bin Abdullah ministan harkokin waje na SaudiyyaHoto: Thomas Koehler/AA/photothek.de/picture alliance

Ukuba da 'yan Gaza ke ciki ba kasancewar ma'aunin tallafa wa al'ummar Falasdinawa a   Gaza, ya sanya hukumomin Berlin kara ba da tallafin Euro miliyan 50 ga Falasdinawa da kuma amfani da mashigin kasar ta Jordan wajen shigar da kayan agajin jinkai zuwa Gaza, inda a kowanne mako motoci sama da 120 ke shiga yankin. Tun bayan barkewar yakin daga ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 Jamus ta kashe sama da Euro miliyan 360 wajen samar da abinci da magunguna da sauran kayan agajin jinkai a Zirin na Gaza.

Annalena Baerbock tare da ministan harkokin waje na Jodan
Annalena Baerbock tare da ministan harkokin waje na JodanHoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

Shi ma ministan harkokin wajen Jordan Ayman Safadi, ya ce akwai bukatar daukin gaggawa wajen warware takaddamar da ke tsakanin Isra'ila da Hamas kafin yakin ya dagule al'amura a yankin Gabas ta Tsakiya. "Ya ce, muna gargadinku kan cewa taba muhimman wuraren ibada a Gabas ta Tsakiya na nufin taba yankin baki daya. Don haka sakonmu a bayyane yake, na bukatar kasashen duniya su tashi tsaye wajen kawo karshen rikicin kafin bakin alkalami ya bushe na tarwatsewar Gabar Yamma da kogin Jordan, wanda hakan ka iya shafar yankin baki  daya.”