Yunkurin Taliban na karbe iko
August 12, 2021Talla
Wasu kasashen Turai sun yanke shawarar dakatar da mayar da 'yan kasar Afghanistan da suka nemi mafaka gida a sakamakon munin fadan da ake da mayakan Taliban. Rahotannin na cewa, a cigaba da yunkurinta na mamaye Afghanistan kungiyar ta karbe iko da binrin Ghazni birni na biyu mafi girma da ke Kudu maso yammacin Kabul.
Masu sharhi dai na ganin faduwar birnin Ghanzni mai tazarar kilo mita 150 kacal daga birnin Kabul, ka iya zama wata kafa ta shigar 'yan kungiyar zuwa Kabul babban birnin Afghanistan.