Afghanistan: Kara karfin ikon Taliban
August 10, 2021A yanzu dai ya zama wajibi Jamus ta taimaka wa ma'aikatan gwamnatin Afghanistan ba tare da bin ka'idar diflomasiyya ba, in ji Sandra Petersmann a cikin sharhin da ta rubuta. Ta ce karyawa inda ba gaba da Taliban ke yi a fagen yaki a Afghanistan, ya sa gaskiya ta fara fitowa fili: Ma'ana Amirka ta gaza cimma burinta a yakin mafi tsawo da ta yi cikin tarihinta tare da gudunmawar kungiyar tsaro ta NATO. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata dai, kungiyar Taliban da ke da kaifin kishin Islama ta yi nasarar karbe manyan larduna da dama na arewacin kasar daga hannun dakarun gwamnati ciki har da birnin Kundus, inda rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr ta kula da tsaro na tsawon shekaru. Tun dai bayan da Amirka da kawayenta na NATO suka janye dakarunsu daga Afghanistan ba tare da wani sharadi ba, kungiyar Taliban ta yi amfani da wannan dama wajen cin karenta babu babbaka.
Karin Bayani: Mayakan Taliban na kara kaimi a Afghanistan
Adadin fararen hula da suke jikkata na dada karuwa, lamarin da ya sa miliyoyin mutane yanke shawarar kauracewa matsugunansu tsakanin watan Mayu zuwa Yuli a cewar Majalisar Dinkin Duniya. Da dama na neman yin hijira zuwa Kabul babban birnin kasar domin samun tsaro, wasu kuma sun kudiri aniyar isa Turai ta makwabtan kasashen Pakistan da Iran.A yanzu dai yakin basasar Afghanistan, wanda aka kasa warware shi tun tsawon shekaru 40 da suka gabata, ya sake danyacewa. Ayar tambaya a nan ita ce: Ya kamata Afghanistan ta zama kasa mai bin tafarkin shari'ar Musulunci ko a'a? Ta ya ya kasar ta samu kanta cikin wadi na tsaka mai wuya? Kawancen da Amirka ta jagoranta ya kasa tattaunawa da Taliban lokacin da ta yi rauni a hunturun 2001. Kasashen yammacin duniya sun yi gaban kansu, inda suka yi watsi da tushen rikice -rikicen Afghanistan tare da gudanar da ayyukan sojoji da na siyasa a kan manufofinsu na cikin gida.
Babban burin da Amirka ta sa a gaba a wancan lokaci shi ne, ramuwar gayya ga hare -haren ta'addanci na 11 ga Satumban 2001 da kuma farauto Osama bin Laden ko ta halin kaka.Ita kuwa Jamus, ta yanke shawarar sake gina Afghanistan tare da bai wa babbar abokiyar huldarta hadin kai domin a guda tare a tsira tare. Wannan ita ce kafar da suka bi wajen bayyana wa talakawansu dalilansu na aikin sojin kasashen waje a Afghanistan. Sai dai kungiyar Taliban ta ninka karfi a yankin iyakar Pakistan da Afghanistan, yayin da kawancen kasashen Yamma ya kulla kawance mai cike da shakku da muggan jagororin yaki, sannan cin hanci da rashawa da cin zarafi ya samu gindin zama a kauyukan kasar. A daya hannun kuma yakin Iraki ya shagalar da masu ruwa da tsaki tare da haifar da sabon nau'in ta'addanci. A takaice dai, bayan shekaru na ta-ci- ba-ta-ci ba, ba a gano bakin zaren warware rikicin Afghanistan ba, duk da mamaye fagen diflomasiyya da sojojin Amirka suka yi.
Karin Bayani: Sharhi kan tattaunawar Amirka da Taliban
Amma daga bisani saboda dalilai na siyasar cikin gida, tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya fara tattaunawa da Taliban cikin bazarar 2018 ba tare da ya hada kai da zababbiyar gwamnatin Afganistan ba, ko la'akari da matsayin abokan hulda na NATO ba. Shi kuwa magajinsa Joe Biden ya tabbatar da ficewar sojojin Amirka ba tare da wani sharadi ba. Dalilin da suka bayar shi ne: Afghanistan ta daina zama barazana a fannin ta'addanci a duniya. Batun sake tura sojojin NATO zuwa fagen daga a Afghanistan bai ma taso ba. Abin da Amirka da kawayenta za su iya yi yanzu shi ne: yin matsin lambar siyasa da ta kudi a kan Taliban, saboda za su bukaci masu gida rana idan sun kakkange madafun iko. Wannan yana nufin yin aiki tare da kasashe masu wuyar sha'ani kamar Pakistan da Iran da Chaina da kuma Rasha. Ta bayyana a fili cewa Taliban ba za ta iya cin wannan nasara cikin hanzari ba tare da taimakon Pakistan ba.
Ita Jamus fa me ya rage mata? Fadar mulkin ta Berlin na da alhakin taimaka wa mutane da suka yi aiki tare da sojojin Bundeswehr da kungiyoyin farar hulan Jamus cikin hanzari. Dalili kuwa shi ne: suna fuskantar kalubale daga masu tsattsauran ra'ayin addini saboda zarginsu da suke yi da yaudara. Har yanzu gwamnatin Tarayyar Jamus na jan kafa wajen ceto wadannan ma'aikata daga halin gaba kura baya siyaki da suka samu kansu a ciki, lamarin da ke zama abin kunya. Wani kuma abin kaico shi ne yadda kasa kamar Jamus da ke bin tafarkin dimukuradiyya ke neman tisa keyar 'yan Afghanistan da aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka, lokacin ne da ya kamata ta ba da umurnin dakatar da korar, ma'ana ta lashe amanta. A cikin kusan wadannan shekaru 20, sojojin Bundeswehr sun cika aikinsu a Afganistan. Amma akwai bukatar gwamnati da majalisar dokokin Jamus su yi karatun ta nutsu kan makudan kudi da zubar da jini da aka yi a Afghanistan. Wannan ne zai sa a kauce wa maimaita kuskuren a sauran ayyukan soja, kamar wanda ke gudana yanzu haka a kasar Mali.