Kotun ICC za ta bude bincike a Najeriya
December 11, 2020Talla
Babbar mai shigar da kara a kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta kasa da kasa wato ICC Fatou Bensouda, ta ce tana da cikakkiyar shedar fara bincike kan kashe-kashen da masu ikirarin jihadi ke yi a arewa maso gabacin Najeriya.
Mai shigar da karar ta kara da cewa shedun da ke gareta a hannu, sun isa a bude bincike kan abin da ke gudana a yankin na arewacin kasar.
Kungiyar Boko Haram ta kwashe sama da shekaru goma tana kisan farar hula da basu ji ba basu gani ba a jihohin Barno da Yobe.
Yankin arewacin na Najeriya na cigaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'ada da masu garkuwa da mutane.