Za a bude Rafah don kayan agaji
October 19, 2023Shugaban Amurka Joe Biden ya cimma yarjejeniya da Isra'ila ta ba da damar shigar da kayan agaji a cikin manyan motoci zuwa Zirin Gaza da ke faman shan luguden wuta daga Isra'ilar, wanda ya tilastawa mutane miliyan guda tserewa daga gidajen su don tsira da rayukansu.
Mr Biden ya cimma matsayar bayan kammala ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu jiya Laraba, tare da tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi, yana mai cewar kayan agajin za su fara isa Gaza a gobe juma'a bayan sun bi ta Masar da kuma Rafah.
Yakin na Gaza dai ya hallaka Falasdinawa fiye da dubu uku tare da jikkata mutane dubu goma sha biyu da dari biyar, yayin da Isra'ilawa dubu daya da dari hudu suka mutu, aka yi garkuwa da wasu dari biyu a Gaza.
Hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bakin shugabanta Martin Griffiths ta ce, mazauna yankin su na cikin mawuyacin hali na bukatar taimako, inda ta roki a ba da damar shigar da kayan agajin da suka hada da ruwa sha da magunguna da kuma makamashin fetur da gas.
A daya hannun kuma, fraministan Birtaniya ya isa Isra'ila domin ganawa da takwaransa Benjamin Netanyahu, kafin ziyartar wasu kasashen yankin.