1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matasa za su taka rawa a babban zabe

February 22, 2019

 A Najeriya masu matsakaicin shekaru za su taka rawa mai tasiri a babban zaben da ke tafe a yunkurinsu na sake mika jan ragamar mulki ga gwamnatin demukradiyya.

https://p.dw.com/p/3Dttu
Nigeria,  Rivers: Anhänger des nigerianischen Präsidenten Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

 A Najeriya yayin da ake shirin fara  jefa kuri’a a babban zaben kasar, muhimman batutwan da dama ne dai ke shirin yin tasiri ga masu shirin zuwa jefa kuri'ar musamman ma masu matsakaicin shekaru duba da tarin alkawullan jama'an da 'yan takara suka yi da zai kai ga talakawan fitowa a yankuna daban-dabam yin don zabe, a yunkurin da suke da shi mika jan ragamar jagorancinsu har na tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Duk da cewa zaben na karshen mako na zama karo na shidda a tarihin siyasar Najeriya tun bayan dawowar kasar kan turbar demukradiyya, masu sharhi na ganin babban zaben na zama irinsa na farko da wasu matasan kasar  masu matsakaicin shekaru da aka haifa a daidai lokacin da iskar demukradiyya ke kadawa, wanda kuma ake kallon za su iya taka rawa a fagen canjin tafiyar siyasa ko dorewarta mulki wanda kuma ake ganin zai iya taka rawa mai matukar tasiri. Sai dai a yain da ake ganin matasan kasar za su taka muhimmiyar rawa wajen fitowa yin zaben na Najeriya a wannan karo, a share daya masu sharhi na cewa wannan zaben na zaman zangon karshe ga wani gungu  'yan kasar da suka share shekaru 50 suna renon dorewar demukradiyya.

Ko da yake ta tabbata da cewa 'yan takara da dama ne ke shirin fafatawa daga jam'iyyu daban-dabam a zaben na karshen mako, masana na ganin cewar ba zai wuce jam'iyyu biyu ba kawai da suka hada da APC da PDP da zau kai labari a zaben na Tarayyar Najeriya.