1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaman sulhu ya kasa magance rikicin da Sudan ke fama da shi

Mouhamadou Awal Balarabe
August 23, 2024

Masu rikici da juna a Sudan sun yi alkawarin ba da damar gudanar da ayyukan jin kai, amma ba tare da amincewa da tsagaita bude wuta ba. Tun watanni 16 ne ake gwabza fada tsakanin bangaren al-Burhane da na Daglo.

https://p.dw.com/p/4jrnd
Janar Abdel Fattah al-Burhan na yawan ganawa da jami'an da ke neman warware brikicin Sudan
Janar Abdel Fattah al-Burhan na yawan ganawa da jami'an da ke neman warware brikicin SudanHoto: picture alliance / Xinhua News Agency

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun kawo karshen tataunawar da aka yi a kasar Switzerland ba tare da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba. Sai dai sun yi alkawarin ba da damar isar da kayayyakin jin kai cikin kwanciyar hankali ta wasu muhimman hanyoyi guda biyu. Tun a watan Afrilun 2023 ne aka fara fafatawa a Sudan tsakanin sojoji Janar Abdel Fattah al-Burhane, da dakarun sa kai na RSF da tsohon mataimakin shugaban kasa Janar Mohamed Hamdane Daglo ke shugabanta.

Karin bayani:Al'amura na kara tabarbarewa a Sudan 

Kungiyoyin agaji na yin tir da cikas da ake fuskanta wajen gudanar da ayyukan jin kai, yayin da sama da mutane miliyan 25 ke fama da matsananciyar  'yunwa.  Ana zargin bangarorin biyu da laifukan yaki da suka hada da jefa bama-bamai a yankunan Sudan da ke da yawan jama'a, inda dubban mutane suka mutu tare da raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu, a cewar MDD.