1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: Ana ci gaba da kai ruwa rana

Ramatu Garba Baba
July 27, 2020

Shugabanin yammancin Afirka 5 ne suka soma wani zaman taro da zummar shawo kan rikicin kasar Mali, inda bangaren jagoran adawa Imam Mahmoud Dicko ke son ganin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/3fylC
Krise in Mali | ECOWAS | Muhammadu Buhari und Boubou Cissé
Hoto: Présidence du Mali

Biyar daga cikin shugabannin kasashen yammancin Afirka sun soma wani taro a wannan Litinin da zummar shawo kan rikicin siyasar kasar Mali. Taron wanda shi ne karo na uku tun bayan tsanantar rikicin, zai mayar da hankali kan samar da maslaha a tsakanin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da jagoran jam'iyyar adawa Imam Mahmoud Dicko.

Matakin shiga tsakani da Shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Cote d'Ivoire da Senegal suka yi, da ma wanda tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya jagoranta duk sun ci tura.

A cewar Kungiyar Ecowas,  ba a fidda zato na cimma matsaya ba duk da cewa sun nuna rashin amincewa da takaddamar muradun masu hamayyar da IBK na ya yi murabus daga mulki ba. Yanzu dai an zura idanu don ganin yadda za ta kaya.