1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da wahalar rayuwa a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
February 6, 2017

Kungiyoyin daban-daban suka jagoranci yin zanga-zangar don nuna bacin ransu da matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/2X3BY
Nigeria Proteste gegen der hohen Ölpreis
Najeriya dai na fuskantar zanga-zangar al'umma kamar a nan lokacin cire tallafin man fetirHoto: Reuters

Kungiyoyin farar hula da ke rajin kare hakin jama'a da demukuradiyya sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu da   matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki da suka ce ana fuskanta a Najeriya, duk da janyewa da fitaccen mawakin nan Tuface Idibia ga jagorantar lamarin, yayin da wasu gungu da ke goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari su kuma suka ja daga a gefe guda.

Kungiyoyin da suka hallara a dandalin 'yanci na Unity Fountain, da ke nuna adawa da yadda Shugaban Najeriyar  Muhammadu Buhari ke jagorantar kasar dai suna dauke da kwalaye da aka rubuta kalamai iri daban-daban na neman lallai gwamnati ta dauki mataki. Professor Chidi Odiankalu fitaccen mai fafutuka a wannan fanni na cikin masu jagoratar zanga-zangar ya bayyana cewa.

"'Yan Najeriya fa na ganin ba a biya masu bukatunsu, 'yan Najeriya na cikin fushi. Idan gwamnati ta fito tana bayani tare da tausawa za mu fahimta. Shugaba Buhari ya yi shiru bai mana bayani a kan yaki da cin hanci da rashawa ba, da batun tattalin arziki. Sai kawai a yi mana barazana da turo mana 'yan sanda, dukkanmu za mu mutu, za su iya harbi na."

'Yan sanda sun ja daga a kusa da dandalin zanga-zangar da ke Abuja
'Yan sanda sun ja daga a kusa da dandalin zanga-zangar da ke AbujaHoto: DW/U.Abubakar Idris

Akwai mata da ke wakiltar kungiyoyi da dama da suka hallara a wajen zanga-zangar duk kuwa da janyewar da fitaccen mawakin nan Tuface Idibia ya yi. Hajiya Fatimah Abba Kaka ta ce yanayin fa ya yi zafi.

"Yara ba makaranta, kudin abinci ka komai ya yi tsada. Canji suka ce mana, kuma gwamnati ba ta mutum daya ba ce, jama'a ita ce gwamnati. Kuma fitowarmu a nan cewa muke gyara abinka ba zai zama sauke mu raba ba."

Sun dai ta rera wakoki da suka bayyana bukatunsu.

Ga Malam Umar Hadejia da ya yi tattaki daga jihar Jigawa ya ce "rashin bayyana gaskiyar lamura shi ya fi tayar masu da hankali."

To sai dai a bangare guda akwai masu goyon bayan shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari da suka yi tasu zanga-zangar. Abdulhamid Abdullahi Dankerko na kungiyar da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Buhari ya ce akwai bukatar nuna fahimtar matsaloli.

"Ya kamata talakawan Najeriya da suka zabi Buhari su yi hakuri. Cani mika ce muke nema kuma mun samu canji. Canjin nan ba a rana daya ake samu. Idan mutum ya fara rashin lafiya ba a rana daya zai samu lafiya ba."  

Amma ga El-Harun Mohammed masani a fanin tattalin arziki da ci gaban kasa na mai cewa "akwai dalili na fuskantar wadannan matsaloli na hauhawar farashin kaya da ma tsadar rayuwa."

Abin jira a gani shi ne mataki na gaba da gwamnatin zat a dauka a kan wannan matsala da  tun ana shagube zuwa ga magana ta kaiga mutane fitowa suna gudanar da zanga-zanga a kai, da kwararru ke cewa lamari ne mai hatsari fa tarayyar Najeriya.