Kano: Yunkurin ci da gumin maniyyata
June 30, 2022Alhazan Jihar Kano 284 ne suka gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin Hukumar alhazai ta jihar domin bayyana fushinsu bisa yadda hukumar ta maye gurbinsu da wasu, bayan da aka sanyasu yin adashen 'yar gata na tsawon shekaru biyu, alhazan sun bayyana cewar ba za su taba aminta da wannan mataki da aka dauka akansu ba, duba da cewar, sun gama tanadi har wasu ma sun yi sallama da iyalansu.
Fusatattun maniyyatan, sun yi dandazo a harabar Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano a arewacin Najeriya, inda suke bayyana takaici bisa yadda mai doki ya koma kutiri, alhazan sun bayyana cewar kusan shekara biyu aka umarcesu da su bude asusun ajiya a bankin Jaiz domin yin adashin 'yar gata da nufin samun kujerar zuwa aikin hajji, amma sai da suka gama tara kudin har aka sa musu lokaci suka kuma cika gibin da ya rage, sai ga shi daga bisani baya ta haihu, inda aka ce musu ba za su sami kujerar ba,
Yanzu haka, wadannan maniyyata na cikin halin dimuwa da rashin tabbas, domin wasu na kukan cewar yaudarar su akayi sai da suka gama saka rai da kuma shiri, sannan aka jefa su cikin wannan yanayi.