1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin almubazzaranci a masarautar Kano

Nasir Salisu Zango
April 24, 2017

Majalisar masarautar Kano a Najeriya, ta mayar da martani dangane da cece-kucen da ake yi na zargin almubazzaranci da ake wa mai martaba sarkin Kanon Muhammadu Sanusi na biyu.

https://p.dw.com/p/2bq2m
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyuHoto: Amino Abubakar/AFP/Getty Images

Tun makwanni biyu da suka gabata dai babban abin da ke jan hankali shi ne batun zargin da ake na cewar an kashe biliyoyin kudi ba bisa kai da ba a masarautar, wanda ya jawo hankalin Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta jihar, har ma ta aike sammaci ga wasu kusoshin masarautar. Sai dai kuma mutane na ganin cewar wnanan bita da kulli ne kawai ake wa masarautar tun bayan sukar lamirin wasu manufofin gwamnati da mai martaba sarkin ya yi, kan batun gina layin dogo a birnin Kano, inda maganganu suka yi ta fitowa da ke zaman suka kai tsaye ga masarautar. Wani abu da ya zama babban abin jan hankali shi ne sukar laimirin yadda aka kashe wasu kudade har naira biliyan shida wadanda aka ce marigayi sarkin na Kano Alhaji Ado Bayero ya bari a cikin asusun masarautar har ma aka bayyana wasu hanyoyi da aka ce an bi wajen kashe su. A dangane da haka a wannan Litinin din 24 ga watan Afrilun da muke ciki, majalisar masarautar Kanon ta bayyana cewar ko kadan Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, bai gaji naira biliyan shida daga tsohon sarki mai rasuwa ba, hasali ma naira biliyan guda da miliyan dari takwas da 'yan kai ya gada, a cewar Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali yayin wani taron manema labarai da masarautar ta gudanar.

Daya daga cikin batun da ya fara janyo cece-kuce, shi ne batun dokar aure da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci a yi.
Daya daga cikin batun da ya fara janyo cece-kuce, shi ne batun dokar aure da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci a yi.

 

Kokari na tsige wa ko dakatar wa

Tun lokacin da aka fara wadannan batutuwa aka yi ta samun labarai da ke nuna cewar ana shirin tsige sarki Muhammadu Sanusi na biyu, haka zalika ma wani taro da gwamnonin arewacin Najeriya ke yi yanzu haka a kasar China yasa an yi ta yada jita-jitar cewar ana kitsa kokarin tsige sarkin ne,  sai dai masarautar ta Kano ta yi watsi da wannan batu. Yanzu haka Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta jihar Kano ta kaddamar da bincike a kan wannan batu. Muhyi Magaji Rimin Gado shi ne shugaban hukumar ya kuma ce aiki suke na bincike kuma ya yi watsi da zargin cewar binciken nasu yunkuri ne na tsige sarki. Mutane da dama dai na ganin cewar bai kyautu a ringa batun tsige sarki ba amma dai ya kyautu sarki ya takaita yawan zantuka da yake.Zuwa yanzu dai babban abin da ke jan hankali shi ne batun binciken da aka fara musamman ma gayyatar da aka yi wa wasu kusoshin masarautar guda biyu.