1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya na cike da rudani

Suleiman Babayo AS
March 9, 2023

Jiga-jigan 'yan adawa a Najeriya sun garzaya kotu kan zargi magudi a zaben shugaban Najeriya yayin da aka jinkirta zaben gwamnoni da mako guda.

https://p.dw.com/p/4OT5B
Najeriya | Masu zabe
Masu zabe a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Manyan 'yan adawa a Najeriya da suka gaza samun nasara nasara a zaben shugaban kasa sun garzaya kotu inda suka kalubalanci sahihancin zaben, yayin da hukumar zaben kasar ta jinkirta zaben gwamnoni da mako guda.