Zelensky ya mika shirin samun nasara kan Rasha
October 17, 2024Shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky, ya sake jaddada neman karin agajin kudi da kudurin shiga kungiyar tsaro ta NATO, inda ya mika shiri mai kunshe da manufofi biyar na samun nasara a yakin da yake yi da Rasha, a taron kungiyar Tarayyar Turai da ke gudana a birnin Brussels. Shugaba Zelensky ya bukaci shugabanin EU da su goyi bayan yunkurinsa na gaggauta amince wa da shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO domin kawar da barazanar Putin.
Karin bayani: Zelensky zai gana da shugabannin EU
Babban Sakataren kungiyar NATO, Mark Rutte ya jadadda matsayar kungiyar na kasancewar Ukraine zama mamba a cikinta sai dai kuma bai bayyana lokacin ba. Tun da fari dai, Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya bayyana cewa, yunkurin neman zama mamba da Ukraine ke yi a NATO shi ne dalilinsa na kaddamar da mamaya a kasar.