1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Angela Merkel a tarayyar Najeriya a matakin ƙarshe na rangadin Ƙasashen Afirka uku

July 14, 2011

Shugabar gwamantin ta Jamus ta gana da shugabannin addinan Musulunci da Kirista don neman ƙarin bayani game da ƙoƙarin da sassan biyu ke yi wajen samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/11vgQ
Hoto: dapd

A ziyarar da ta kai tarayyar Najeriya, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da shugabannin addinan Musulunci da Kirista na Najeriya inda ta nemi ƙarin bayani game da irin matakan da sassan biyu ke ɗauka wajen samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu, kasancewar ana yawaita samun rigingimun dake da nasaba da addinai da kuma na ƙabilanci a ƙasar.

Rikice rikicen addini da na ƙabilanci na barazanar zama ruwan dare a tarayyar Najeriya, inda yanzu haka da wuya a wayi gari ba tare da samun labarin aukuwar wani rikici dake da nasaba da addini ko ƙabilanci ba. Waɗannan rigingimun da kuma taɓarɓarewar yanayi tsaro suna baraza ga ɗorewar kyakkyawar zamantakewa tsakanin al'umomi daban daban a tarayyar ta Najeriya. Akan haka a ziyarar da take yi a Najeriya, shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta gana da shugabannin addinin Muslunci da na Kirista a birnin Abuja, inda ta nemi ƙarin bayani game da ƙoƙarin da shugabannin addinan guda biyu ke yi domin zaman lafiya da fahimtar juna su wanzu.

Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar na uku shi ya jagoranci tawagar musulmi a tattaunawar da shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel, to sai dai duk ƙoƙarin da muka yi mu same shi ta wayar tarho ya ci-tura. Amma Ustaz Musa Mohammed Limamin masallacin Juma'ar Abuja wanda shi ma ya halarci taron cewa yayi sun gamsu da ganawar da shugabar gwamnatin ta Jamus.

Horas da malamai masu wa'azi na ɓangarorin Musulmi da Kirista yana da muhimmancin gaske domin idan ba su ƙoshi da ilimin kuma ba su fahimci koyarwar addininsu ba to za su iya ɓatar da jama'a. Archbishop Ignatius Kaigama da shi ma ya halarci taron ya ce rashin isasshen ilimin shi ke sa ake amfani da addini wajen tayar da fitina maimakon kwanciyar hankali da zaman salama.

Najeriya dai ƙasa ce mai al'umomin da kuma addinai daban daban kuma sai an san da haka ne za a iya magance abubuwan da ka iya tasowa waɗanda suka shafi Musulmi da kuma Kirista. Uszaz Musa Mohammed ya ce rashin adalci daga ɓangaren hukumomi na daga cikin abubuwan dake ta da fitinu a cikin ƙasa.

Archbishop Ignatius Kaigama ya yi fatan Jamus za ta ba da gudunmawa domin a ci-gaba da irin wannan tattaunawa.

Ko shakka babu ganawar tsakanin Angela Merkel da shugabannin addinan ba zai rasa nasaba da damuwar da ɗaukacin kamfanonin Jamus dake sha'awar zuba jari a Najeriya ke nunawa game da tabarbarewar halin tsaro a wasu yankunan kasar ba wanda ke kawo ciƙas wajen tafiyar da aikin ci-gaban ƙasa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal