Ziyarar Ban Ki Moon a Najeriya
May 23, 2011Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kira ga ɗaukar matakan warware matsalar mace-macen ƙananan yara sakamakon cututtukan daya ce za'a iya shawo kan kansu. A lokacin da ya ziyarci wani asibitin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki alhakin tafiyar dashi a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya, Ban Ki Moon ya ce duniya ba za ta lamunci tsarin kula da lafiyar da a ƙasashe da dama baya biyan buƙatun mata da kuma ƙananan yara ba, yana mai cewar babu wani dalilin amincewa da yanayin da kimanin mata dubu ɗaya ne ke mutuwa a duniya a kowace rana ko dai a wajen haihuwa ko kuma saboda juna-biyu.
Hakanan ya bayyana buƙatar ɓullo da dabarun shawo kan matsalar nan da ta shafi ƙananan yara kimanin dubu 20 dake mutuwa a kowace rana gabannin cika shekaru biyar da haihuwa. Wannan dai ita ce ziyara ta farkon da Ban Ki Moon ya kai Nijeriya tun bayan kama aiki a shekara ta 2007, wadda kuma ya isa ƙasar bayan halartar bukin rantsar da shugaban Cote d'Ivoire Allasane Ouattara, inda kuma ake sa ran zai wuce zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia a wannan Talatar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal