Merkel na son karfafa hulda da Afirka
August 31, 2018Jaridar Farnkfurter Allagemeine Zeitung a sharhin da ta rubuta tana mai cewa ta ce babban batun da ya dauki hankali a ziyarar da shugabar gwamnati Angela Merkel ta kai kasashen Senegal da Ghana da kuma Najeriya a wannan makon shi ne yadda za a magance musabbabin kaurar da matasan Afirka ke yi zuwa Turai. Jaridar ta ce shekaru uku bayan da Merkel ta bude kofofin Jamus ga dubun dubatan 'yan gudun hijira, yanzu hanalin Jamus da ma Turai ya tashi game da wata sabuwar hijirar al'umma daga Afirka, domin sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasashen Afirka ya nuna cewa kimanin kashi daya kashi biyu na matasan Afirka na da burin yin kaura zuwa Turai, saboda rashin hangen wata makoma ga rayuwarsu a Afirka.
Matsaloli na rashin shugabanci na gari da cin hanci tsakanin shugabanni da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasa da sace dukiyar kasa na daga cikin abubuwan da ke jefa rayuwar 'yan Afirka cikin mawuyacin hali. Sai dai a cewar jaridar duk wani taimako da Turai za ta ba wa Afirka zai yi tasiri ne idan gwamnatocin Afirka suka ba da tasu gudunmawa wajen aiwatar da kyawawan tsare-tsare da samar da kyakkyawan yanayi na siyasa da zuba jari da uwa uba yaki da cin hanci a rashawa.
Bunkasa huldar kasuwanci da Afirka
Huldodin kasuwanci a matsayin jigo a ziyarar Merkel zuwa kasashe uku na yammacin Afirka inji jaridar Berliner Zeitung. Jaridar ta ce Senegal, Ghana, Najeriya, kasashe uku a cikin kwanaki uku a rangadin da Merkel ta fara ranar Laraba, inda batun fadada huldodin kasuwanci ya dauki sahun farko.
Magance kaurar matasan Afirka zuwa Turai
Manufa ita ce kasashen Afirka za su iya samun sahihar demukuradiyya da kwanciyar hankali ne kawai idan al'ummomin wannan nahiya suka samu kyakkyawar makoma. Tun ba yau ba gwamnatin Jamus ke bin tsarin hulda irin ta aboki da aboki da nahiyar Afirka, domin ta san irin fa'idojin da za ta samu idan nahiyar Afirka da ke zama makwabciya ga nahiyar Turai, ta tsaya a kan kafafunta.