Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus A Yankin Gabas Ta Tsakiya
September 1, 2004A gobe alhamis ne idan Allah Ya kaimu Joschka Fischer zai sadu da sauran takwarorinsa ministocin harkokin wajen kasashen Kungiyar Tarayyar Turai domin ya labarta musu sakamakon shawarwarin da ya gudanar a ziyarar tasa ga Yankin Gabas Ta Tsakiya. A dai wannan marra da ake ciki babu wata alamar dake nuna cimma bukatar da ministan harkokin wajen na Jamus ya gabatar a game da lafar da kurar rikici tsakanin Isra’ila da Palasdinawa domin zama sharadin zaman lafiyar Yankin Gabas Ta Tsakiya. A bangare guda ba a hangen wani takamaiman mataki na garanbawul ga mahukuntan Palasdinawa, sannan a daya bangaren kuma shingen da Isra’ila ke ginawa a kuryar yankunan Palasdinawan na mummunan karantsaye game da aiwatar da shirin zaman lafiyar nan na sabuwar taswira. A baya ga haka ziyarar Fischer ga kudancin Isra’ila tayi kacibis da fashewar wasu bamabamai guda biyu a motocin safa tare da sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma kara dagula yanayin da ake ciki a Isra’ilar. Abu daya dake ba da kwarin guiwa shi ne shirin da P/M Isra’ila Ariel Sharon ya zayyana na janye Yahudawa ‚yan kaka-gida kimanin dubu 75 da dukkan sojojin dake ba su kariya daga zirin Gaza. Duk da adawa mai tsanani da yake fuskanta daga jam’iyyarsa, amma Sharon ya dage akan wanzar da shirin nasa nan da karshen shekara ta 2005. Wannan janyewar ka iya zama wani sahihin mataki na farko akan hanyar neman zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinawa, kamar yadda Fischer ke gani, amma fa ya ce tilas ne matakin ya hada da dukkan yankunan Palasdinawan dake karkashin mamayen Isra’ila, ba zirin Gaza kadai ba. Domin kuwa manufar shirin zaman lafiyar nan na sabuwar taswira, wanda aka gabatar a hadin guiwa tsakanin Amurka da Rasha da MDD da KTT, shi ne samar da ‚yantattun kasashe biyu da zasu wanzu kafada-da-kafada da juna, kuma ba zata yiwu a kayyade wa Palasdinawa yankin Zirin Gaza kadai ba, wajibi ne kasar ta su ta hada har da yammacin gabar kogin Jordan. Amma abin takaici ana ci gaba da fadada matsugunan Yahudawan kimanin 150 da aka giggina a wannan yanki tare da goyan baya daga Amurka, wacce ba za a iya kwatanta ta tamkar mai neman sasantawa tsakani da Allah ba, a maimakon haka take rufa wa Isra’ila baya a manufofinta na yada angizo. Kasashen Turai dai sun dogara ne akan kasar Amurka, wacce ke ruwa da tsaki a Yankin Gabas Ta Tsakiya, duk kuwa da cewar rikicin yankin ya fi shafar kasashen Turai saboda makobtakarsu kai tsaye da juna. Amma Isra’ila ba zata yarda ta saurari ta bakinsu ba, musamman ganin yadda ake dada samun karuwar manufar kyamar Yahudawa a kasashen na Turai. Wani abin da ka iya taimakawa shi ne, idan kasashen sun sa baki domin dakatar da shirin Iran na makaman nukiliya. A dai halin yanzu haka kasashen Birtaniya da Faransa da ita kanta Jamus, kamar yadda ministan harkokin wajenta ya nunar, suna shirin taimaka wa Iran da fasahar nukiliya domin amfanin farar fula, lamarin da ba shakka yake ci wa Isra’ila tuwo a kwarya.