Ziyarar shugaban Jamus a Gabas ta Tsakiya
November 30, 2010Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Jamus na da rawar da za ta iya takawa wajen warware rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin Gabas ta Tsakiya. A lokacin da ya gana da shugaban Tarayyar Jamus Christan Wulff a birnin ƙudus, Netanyahu ya ce Tarayyar Jamus za ta iya taimakawa a samu fahimta tsakanin Isra'ila da sauran ƙasashen yankin da suke taƙaddama da ita.
Sai dai shugaba Wulff ya jaddada matsayin ƙasarsa a inda yayi kira ga ɓangarorin da ke gaba da juna da kai hankali nesa, tare da neman Isra'ila ta dakatar da gine-ginen wuraren share wuri zauna a zirin Gaza, da sune ummal'aba'isan cijewar tattaunawa. Firaminista Netanyahu na Isra'ila ya nunar da cewa a shirye ya ke ya koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da palesɗinawa.
A yau ne shugaba Wullf zai gana da shugaban Palesdinu wato Mahmoud Abbas a ci gaba da rangadin kwana huɗu da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou