1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a ƙasar India

October 30, 2007
https://p.dw.com/p/C15O

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka birnin New Delhi domin fara ziyarar aiki ta kwanaki huɗu a ƙasar India. Maƙasudin ziyarar dai ita ce domin bunƙasa dangantakar diplomasiya dana cinikayya a tsakanin ƙasashen biyu. A yau talata shugabar gwamnatin zata gana da shugaban ƙasar Indian Pratibha Patil da kuma Firaminista Manmohan Singh. Ana sa ran zata yi amfani da ganawar ta da Firaminista Manmohan Singh domin tattauna muaámala ta cudanni- in cude ka ta fannin binciken kimiya da kuma batun dumamar yanayi. Da yake jawabi jim kaɗan bayan saukar shugabar gwamnatin ta Jamus, Firaminstan India Manmohan Singh ya yaba da namijin ƙoƙarin Angela Merkel wajen jawo hankalin ƙasashen duniya su haɗa ƙarfi wuri guda domin fuskantar sauyin yanayin muhalli. Ziyarar ita ce ta farko da Merkel ta kai ƙasar India tun bayan da ta hau karagar mulki a shekarar 2005.