1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Yawan zuwa asibiti a waje na tada kura

Ubale Musa Abdoulaye Mamane(ATB)
November 2, 2022

A daidai lokacin da miliyoyin 'yan Najeriya ke kokarin yanke hukuncin zabe sabon shugaba, batun lafiyar shugabannin kasar na cigaba da daukar hankali.

https://p.dw.com/p/4IyrC
Cece-kuce game da batun lafiyar shugabannin Najeriya
Cece-kuce game da batun lafiyar shugabannin NajeriyaHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Ya zuwa yanzu Shugaba Buhari ya kafa tarihin zama mafi yawan ziyarar kasashen waje don neman lafiya, inda a cikin shekaru bakwai da rabin da ya shafe kan mulki ya ziyarci kasar Ingila har sau takwas a wani abun da ke kara fitowa fili da kalubalen da kasar ke fuskanta. Najeriya ta fara hasashen irin mutanen da ke shirin gadon Shugaba Buhari, game da batun lafiya inda biyu daga cikin masu takarar shugabancin kasar hudu sun haura shekaru 70, a yayin da kuma ragowar guda biyun suka haura 60 a wani abun da ke kara fitowa fili da auren tarrayar Najeriyar da sabon tsoho a nan gaba.

Karin Bayani: Rudani a fagen siyasar Najeriya 

Kama daga batun rashin tsaro zuwa ga durkushewar tattalin arziki, shugaban na da bukatar rage bacci da kila ma jin dadi kafin iya kai wa ga cika alkawarin da ke tsakaninsa da al'ummar kasa. Batun gazawa ta fannin kiwon lafiyar dai na da ruwa da tsaki a nuna gazawa wajen cika alkawarin gwamnatocin kasar kama daga Umaru Musa Yar’Adua da ya rasa ransa yana kan karagar mulki har zuwa ga shi kansa shugaban kasar da ke ci yanzu wanda ake wa kirari na baba go slow.

Hoton barkwanci kan tafiye-tafiyen shugaban kasa Muhammadu Buhari
Hoton barkwanci kan tafiye-tafiyen shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ko ya take shirin ta kasance a tsakanin dattatwan da ke shirin mulki ga kasar da kuma miliyoyin 'yan kasar masu karatun sauyi, ga daya dan takarar da ke neman karbar mulki a hannun shugaban Sanata Rabiu Musa Kwankwaso "Ba wata hujjar yawon duniya da nufin nema namagani ga shugabannin Najeriya". Sai dai Sanata Olurombe Mamora karamin ministan lafiya a gwamnatin tarayya, fitar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi waje binciken lafiyarsa ba ta da laifi a tsari.

Karin Bayani:  Najeriya: Kara karfin aljihun 'yan siyasa

"Babu wani lokacin da mutane ba za su fita zuwa waje ba, a wani lokaci ma batu ne na neman shawara daga kwarrarun likitoci, wani zai ba da shawarar yi maka tiyata wani kuma zai ce ba ka bukatar wannan. Ina ba ka tabbacin cewar tsari na lafiyarmu na inganta, musamman ma bayan abun da muka samu a lokaci na annobar Covid".

Karamin ministan a ma'aikatar lafiya ta Najeriya ya ce dalilan da suka sa Shugaba Buhari ya fita waje ganin likita dalilai ne da suka shafi shugaban, wata kila ya je ne don duba inda aka kwana game da lafiyar jikinsa, amma kuma muna da kwarewa duk da yake ba ma da kayan aiki isassu, sai dai kuma muna samun kwakkwaran ci gaba.