Salon rayuwa
Ƙeƙe da Ƙeƙe: Makomar Ilimi bayan zaben Najeriya
M. Ahiwa
December 7, 2022Talla
Batun ilimi a Najeriya, na ci gaba da daukar hankali musamman tunanin 'yan kasar game da makomarsa a sabuwar gwamnatin da ake sa ran kafawa bayan zaben da ke tafe na 2023. Shakku game da makomar ilimin dai, ya kara fitowa fili ne ganin yadda a wannan gwamnat mai ta APC, malaman jami'o'in gwamnati suka yi yajin aiki har na tsawon watanni takwas da ya sha dalibai baya matuka.