Abokin hamayyar al-Sisi ya jefar da kwallo a zaben Masar
October 13, 2023Daraktan yakin neman zabensa ne ya sanar da cewa al-Tantawi bai yi nasarar tattara sa hannun 'yan kasa 25,000 da ake bukata don samun damar tsayawa takarar zaben shugabancin Masarba, duk da goyon baya da yake da shi a kasar. Sai dai an kama kimanin magoya bayan wannan tsohon dan majalisar mai shekaru 44 da haifuwa a lokacin yakin neman zabe. Sannan al-Tantawi ya zargi Jami'an tsaro da sanya na'urar leken asiri a cikin wayarsa.
Karin bayani: Jama'a sun kauracewa rumfunan zaben Masar
Baya ga Shugaba Abdel Fattah al-Sissi da ya tattara sa hannun 'yan majalisa 424, 'yan takara uku da ba sa da karfin fada a ji ne za su yi zawarcin kujerar shugabancin Masar, ciki har da Farid Zahran da Abdel-Sanad Yamama da Hazem Omar. Daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Disamba ne al'ummar Masar za su kada kuri'a, amma matsin tattalin arziki zai kasance babban batu a zaben kasar da kashi biyu bisa uku ke fama da talauci.