Makomar Afghanistan a mulkin Taliban
August 19, 2021Makwanni biyu gabanin kammala ficewar sojojin Amirka da suka kwashe tsawon shekaru 20 a kasar ta Afghanistan din ne dai, mayakan na Taliban suka danna fadar gwamnati da ke birnin Kabul tare da kwace mulki. Tun dai da Amirkan da sojojin kungiyar tsaro ta NATO, suka bayyana aniyar kammala ficewa daga kasar zuwa karshen wannan wata na Agusta da muke ciki ne, aka fara shiga fargaba da rudani na rashin tabbas kan halin da kasar za ta iya tsintar kanta a ciki.
Sojojin Amirkan na fara tattara komatsansu da kuma fita daga kasar, mayakan Taliban suka fara fadada ikonsu ta hanyar karbe manyan gundumomi. Cikin kwanaki kalilan ne kuma, Taliban din ta kwace birnin Kunduz da ke zaman birni na biyu mafi girma a kasar ta Afghanistan. Kwace Kunduz din dai, ya sanya tunanin cewa gwamnatin ta Afghanistan na daf da rushewa. Tuni dai al'ummomin kasa da kasa, suka fara kwashe 'yan kasarsu da ke Afghanistan da kuma kiran a kiyaye hakkokin dan Adam musamman ma na mata, abin kuma da Taliban din ta yi alkawarin kiyaye wa bisa koyarwar shari'ar da take shirin sake kafawa.