Afghanistan: Kalubalen nasarar Taliban
August 18, 2021A yayin da kasashen yamma na Turai suka koma gefe tare da dokin ganin yadda al'amura za su kasance bayan Taliban ta karbe madafan iko a kasar Afghanistan, a daya hannun su ma kungiyoyin IS da al-Qaida da wasau kungiyoyi na tarzoma na lura da halin da ake ciki a wannan kasa da ake ganin ta shiga rudani.
Karin Bayani: Al'amura sun fara lafawa a Afghanistan
Guido Steinberg kwararre ne a kan batutuwan da suka danganci yankin Gabas ta Tsakiya a cibiyar nazarin harkokin tsaro da ke Jamus: "Ta bayyana sarai cewa masu ikirarin jihadi 'yan Salafiyya masu tsananin kishin Islama a duk faɗin duniya suna kallon abubuwan da ke faruwa, kuma za su ga nasarar mayakan Taliban a matsayin abun karfafa musu gwiwa. A halin yanzu, ba za ma a san inda wannan zai yi tasiri a zahiri ba. Sai dai akwai wasu wuraren da masu jihadin ke da karfi sosai. Kuma wannan ya hada da Afghanistan din ita kanta".
Kwararru kamar Steinberg na ganin cewa, a kwai sarkakiya dangane da abubuwan da kungiyoyin IS ko ISIS da al-Qa'ida suka aikata a baya da ma wanda suke yi a halin yanzu. IS dai na da yankunanta a Afghanistan da Caucasus da Afirka da Yemen. Sai dai kungiyar ba ta shiri da al-Qaeda da Taliban. Abun da ke nuni da cewar, kafuwar Taliban a Afganistan ba ta nufin IS ma za ta samu karfi. Sai dai hanya daya da za ta karfafa kungiyoyin ita ce kawance kamar yadda a Yemen ga misali babu fada tsakanin al-Qa'ida da IS, a cewar Jassim Mohamad mai binciken ayyukan ta'addanci a cibiyar nazarin yaki da ayyukan tarzoma na Turai da ke Jamus da Netherlands.
Karin Bayani: Rudani bayan Taliban sun kwace ikon Afghanistan
Tun daga shekara ta 2001 zuwa yanzu an samu karuwar kungiyoyin tarzoma a sassa dabam-dabanm na duniya, wadanda a wasu lokuta ke yawaita samun sabani a tsakaninsu. To sai dai a yayin da kungiyar IS ke muradin fadada daularta zuwa wajen yankin Gabas ta Tsakiya, Taliban ta shirya tsaf domin kafa masarautarta cikin Afganistan. Hakan kuma ba zai rasa nasaba da cewar dukkaninsu 'yan asalin wannan kasa ba ne. Sabanin yadda kungiyar take a 2001, sun yi aiki sosai kan muradunsu na siyasa.
Kuma ko shakka babu akwai yiwuwar suna tuntubar kasashen Rasha da Iran da Pakistan, wadanda su ne kasashen da ke ba su tallafin kudi. Yanzu haka dai duniya ta sanya idanu domin ganin ko shin Taliban za ta bai wa marada kunya ta hanyar zama jam'iyyar siyasa abun dogaro kuma wadda za ta iya shiga lamuran kasa da kasa a Afghanistan din? Sai dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ke da shakku kan hakan, ya roki hadin kan kasashen duniya wajen tabbatar da cewar Afghanista ba ta sake zama dandalin sheke ayar kungiyoyin ta'adda ba.