Rudani bayan faduwar gwamnati
August 16, 2021Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci ka da a yi watsi da al'ummar Afghanistan, bayan da mayakan Taliban suka sake kwace iko da kasar. Kwamitin ya yi wannan kiran ne, a yayin wani taron gaggawa da ya gudanar karkashin jagorancin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres kan halin da Afghanistan din ke ciki.
Yayin da yake jawabi a taron gaggawar, Antonio Guterres ya bukaci al'ummomin kasa da kasa da su yi magana da murya guda kan batun take hakkin dan Adam bayan da mayakan Taliban suka sake darewa kan madafun iko.
A yayin da kasar Afghanistan ta tsinci kai cikin wani yanayi na rashin tabbas, a daya bangaren, gwamnatin Jamus tare da wasu manyan kasashen duniya, sun yi kira ga Kungiyar Taliban da ta kwace iko, da ta mutunta ‘yancin dan adam ta hanyar kare rayukan al’ummar kasar, sama da mutum miliyan daya sun tsere daga cikin kasar bisa fargabar yadda rayuwa za ta kasance a karkashin mulkin Taliban.
A halin da ake ciki yanzu, dubban fararen hula na cikin rudani tun bayan da mayakan Taliban suka kwace ikon kasar Afghanistan. Rahotanni sun nuna yadda ‘yan Taliban suka koma aikin binciken shingaye da a baya sojojin gwamnati ke yi. Wasu sassan kasar na zaune lafiya amma akwai wurare da suka hada da filin jirgin saman kasar, da mayakan ke harbin iska domin tarwatsa dandazon jama’a.
Karin Bayani: Sharhi: Taliban na cin karenta babu babbaka
A nata bangaren, gwamnatin Iran ta daura alhakin kwace mulki da Taliban ta yi a kan gazawar rundunar sojin Amirka a yayin da Washington ke zargin gwamnatin Iran din, da marawa mayakan Taliban baya a lokacin da ta ke kokarin murkushe Taliban a tsawon lokacin da rundunar kawance ta kwashe tana yaki da su. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Joe Biden ke shirin yin jawabi kan halin da Afghanistan ke ciki.
Karin Bayani: Afghansitan: Janye sojojin Amirka da NATO
Kasashen yammacin duniya na ci gaba da kwashe jami'an diplomasiyyarsu daga birnin Kabul na Afghanistan, bayan kwace iko da kasar baki daya da dakarun Taliban din suka yi. Tsohon shugaban Afghanistan Asharaf Gani wanda ya fice daga birnin Kabul a gaggauce an tabbatar da cewar ya isa a Tajikistan. Jama'a dai na yin tururuwar ficewa daga kasar saboda fargabar fuskantar cin zarafi.
A wannan Litinin, manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a Afghanistan Ghulam Isaczai ya nunar da cewa rayuwar miliyoyin al'umma na cikin hadari. Tun bayan da Taliban din suka karbi ragamar fadar shugabana kasa.
'Yan Taliban wadanda suka yi mulki daga shekara ta 1996 zuwa 2001 kafin faduwarsu sakamakon harin 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001 saboda goyon bayan da ake zarginsu da bai wa kungiyar Al-Qaida. Masu aiko da rahotannin na cewar janyewar dakarun kasashen duniya daga Afghanistan din ya taimaka wajen samun nasararsu