Kano: Akwai sauran tsalle a shari'ar masarauta
July 15, 2024Sai dai lauyoyin wadanda aka yi kara sun ce har yanzu fa akwai sauran rina a kaba, domin an kashe maciji ne ba a sare masa kai ba. Kotun karkashin Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta bayyana cewar, majalisar dokoki na da ikon yin doka haka shi ma gwamna na da hurumin sanya hannu domin tabbatara da dokar. Ta ce lauyoyin masu kara sun gamsar da kotu cewar wadanda ake kara sun rasa rawunnansu na sarauta, dangane da haka ta ce kar ma su kara ayyana kan su a matsayin sarakuna kuma ja kunnen jami'an tsaro musamman 'yan sanda kan yadda suka bijire wa umarnin da ta bayar a baya.
Yayin da lauyan gwamnati da majalisar dokokin jihar Kano Barrister Ibrahim Isa Wangida ya bayyana gamsuwa da hukuncin, a nasa bangaren lauyan wadanda aka yi karar Barrister Hassan Tanko Kyaure ya ce har yanzu da sauran tsalle domin za su daukaka kara. Shi kuwa Farfesa Mamman Lawal Yusufari da ke zaman lauyan Sarki Aminu Ado Bayero ya ce ya yi mamakin hukuncin, domin tuni suka bayyana janyewarsu daga shari'ar. Wannan maganar ta kotu kan batun sarakuna ta dade tana wata gan-gano a jihar ta Kano, lamarin da a yanzu magidanta kamar Abubakar Ibrahim ke cewar ya kamata a kawo karshen wannan jan-jani. Ga alama dai wannan ba shi ne karshen wannan matsala ba, la'akari da ikirarin daukaka kara da wadanda abin ya shafa suka yi. Wannan kiki-kaka na wanzuwa ne, a daidai lokacin da talakawa ke kuka da yunwa da fatara.