Aljeriya ta dakatar da ayyukan raya kasa a Nijar
January 4, 2024Shirin raya kasashen Afirka na kasar Aljeriya wanda ke gudana a karkashin wata gidauniya mai kunshe da biliyoyin kudade ya tanadi bayar da bashi ga kasashen Afirka, ko tallafa masu ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa da zuba jari a cikinsu. Sai dai a yanzu gwamnatin Aljeriya ta dauki matakin cire kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da Guinea Conakry da Moritaniya daga jerin kasashen da za su ci moriyar shirin nata.
Karin bayani:Nijar ta bude kofofin cinikayya da arewacin Afirka
Aljeriya na zargin kasahen musamman na sabon kawancen AES da ya hada Nijar da Mali da Burkina Faso da ke neman karfafa huldar kasuwanci da ta diflomasiyya da kasar Maroko, wacce ke zama babbar abokiyar gabarta a kan goyon bayan da take bai wa masu neman ‚'ancin gashin kai na yankin Polisariyo. Bana Ibrahim, fitaccen dan fafutika da ke goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, ya ce wannan ba abin damuwa ba ne kuma akwai hanyar da Nijar za ta mayar wa da kura aniyarta.
Karin bayaniMaroko za ta karfafa kasuwanci da kasashen Sahel uku:
Wasu 'yan Nijar sun danganta matakin Aljeriyar da takun sakar da ta shiga da kasar Mali da tasirin da mahukuntan Mali ke yi kan sabbin mahukuntan Nijar., a cewar Siraji Issa na kungiyar farar hula ta Mojen. Shi kuwa Boubacar kado da ke zama masanin tattalin arziki kana mai sharhi kan harkokin siyasa da diflomasiyya a Nijar cewa ya yi akwai mwata fargabar ta daban a cikin lamarin.
Karin bayani: Aljeriya: Warware rikicin Nijar ta diflomasiyya
Kawo yanzu, gwamnatin mulkin sojan Nijar ba ta ce uffan kan wannan matakin na kasar Aljeriya ba, wanda ya zo a daidai lokacin da kasar ke neman karfafa huldar kasuwanci da ita don iya amfani da tashar ruwan Algers wajen shigo da kaya ko kuma fita da su zuwa ketare.