Amirka na fama da karancin malamai
December 5, 2023.A cikin wani rahoto da cibiyar kididdiga da kuma nazarin makaratun gwannati ta kasa ta fitar, ta ce a halin yanzu kashi 86 cikin dari na makarantun suna da karancin malamai. Bayan duba wasu makarantun firamare zuwa na babbar Sakandare fiye da dubu daya da 300 a fadin kasa, cibiyar ta gano cewa, tara cikin 10 na makaratun gwamnati, suna neman malamai wurjajan; musanman a darussan kimiyya, da na koyar da harsunan ketare.
Dalilan karancin malaman a Amurka ya fara bayan annobar corona
Wasu majiyoyi suna cewa, akwai makaratun da a yanzu suke yin karatun kwana hudu cikin sati a maimakon biyar, saboda karancin malamai. Babban dalilin baya-baya da ya haddasa wannan matsala, shi ne, rayukan da aka rasa a lokacin annobar corona, da sabawa da yin aiki daga gida, don haka, wasu malaman, suka gwammace su bar aikin.Bukatar agajin gagawa ga al'umma zai karu