Amurka ta kai hare-haren daukar fansa a Iraki da Siriya
February 3, 2024Fadar White House ta ce a daren Juma'a wayewar Asabar jiragen yakinta sun kai jerin hare-hare 85 a sansanonin sojan Iran daban-daban har duga bakwai da suka hadar da uku a Iraki da kuma hudu a Siriya inda suka halaka kwamandoji da dama.
Karin bayani: Amurka ta sha alwashin ramuwar gayya ga wadanda suka halaka sojojinta a Jordan
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Siriya ta bayar da rahoton cewa akalla mayaka masu samun goyon bayan Iran 18 ne suka halaka sakamakon hare-haren, sannan kuma wasu majiyoyin tsaro sun ba da tabbacin cewa an yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren kungiyoyi masu alaka da Iran a Yammacin Iraki kusa da iyakar kasar da Siriya.
Hukumomin Bagadad sun yin tir da keta haddin kasar domin kai wadannan hare-haren, sai dai daga nata bangare Amurka ta yi ikirarin cewa ta sanar da su kafin ta kai samamen.
Karin bayani: Amurka da Burtaniyya sun kai harin bama-bamai kasar Yemen kan 'yan tawayen Houthi
Dama dai bayan harin na ranar Lahadi 28.01.2024 wanda ya yi ajalin sojojin Amurka uku tare da jikkatar wadansu 30, shugaba Joe Biden ya yi alkawarin daukar fansa kan wadanda suka aikata wannan kuskure da ya sifanta da ''Aika-aika''.