Najeriya ta kara kasafin kudi
October 31, 2023Gwamnatin Najeriya da karo na biyu kenan tana gabatarwa da ma amincewa da kwarya kwaryar kasafin kudin tun daga lokacin da ta hau kan Mulki a watan Mayun shekarar nan. A wannan karon gwamnatin ta zayyanu aiyyukan da ta ce sun zama wajibi ta gudanar da su da suka hada da kudin albashin malaman jami'o'i da na tallafi da za'a rarrabawa ‘yan kasar da ma zabubbuka gwamnonin a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa, inda gwamnatin ta amince da kasafin kudi na Naira tirliyan 2.17. Senator Abubakar Atiku Bagudu shi ne ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya, wanda ya ce haka ya ba da damar aiwatar da bukatun da suka taso.
Karin Bayani: Najeriya: Buhari ya amince da kasafin 2023
Amincewa da dan karamin kasafin kudi dai na nuna hali da tattalin arzikin kasar ke ciki inda take ciwo bashi domin gudanar da muhimman aiyyuka ciki har da rarrabawa yan kasar kayan tallafi bayan janye tallafin farashin mai. Dr Isa Abdullahi masani a fanin tattalin arziki da ke Najeriya ya bayyana bukatar gudanar da gyara a kan yadda ake tafiya.
To sai dai gwamnatin na bayyana dalilai na musamman da suka sanya lamari zama dole a dauki mataki na amincewa da dan karamin kasafin kudin a dai dai lokacin da shekara ta 2023 ke karewa. Abin da yafi daukan hankali shi ne batun kayayyaki tallafi da yadda aka rarraba su musamman mikawa gwamnonin jiho, lamarin da ke cikin kasafin kudin.
Ana nuna damuwa a kan yadda ake tafiya a yanzu a Najeriyar, kasar da ta ci gaba da karbo basussuka daga kasashen waje don gudanar da aiyyuka a kasar ciki har da wadanda in an kashe babu hanyara dawowar kudin kai tsaye zuwa asusun gwamnati.