Ana shirin bude taron kasashen BRICS a Rasha
October 22, 2024Shugabannin kasashen duniya 24 sun hallara a Rasha a ranar Talata domin bude taron kungiyar kasashen BRICS da tattalin arzikinsu ke bunkasa wacce kuma ke neman zama kishiya ga kasashen Yamma. Wannan shi ne babban taron da Rasha ke karbar bakoncinsa tun bayan fara yaki da Ukraine.
Ana ganin ganin shugaban kasar Vladimir Putin na so ya nuna wa kasashen yamma cewa ba su samu nasara ba a kokarin mayar da kasarsa saniyar ware a duniya.
Karin bayani:BRICS: Ajantina ta yi watsi da tayin shiga
Ana sa ran shugaban China Xi Jinping da firaministan Indiya Narendra Modi da kuma shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da duk suka kasance kawayen Rasha za su halarci taron da zai gudana a birnin Kazan daga yau 22 zuwa 24 ga watan Oktoba.
Amurka ta na nuna damuwa kan yadda Moscow ke yaukaka harkokinta na diflomasiyya a yayin da take yaki da kasar Ukraine.
Karin bayani:Shugaba Xi Jinping na China zai kai ziyara kasar Rasha
Wannan taron na BRICs shi ne na 16 da kungiyar ta ke gudanarwa a lokacin da take kara samun mambobi daga kasashen duniya. BRICS na da muradin karya mamayar da dala ta yi a kasuwannin duniya da kuma manufar bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa.