1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAngola

Angola: Ina kudin Isabel dos Santos?

August 22, 2024

Kungiyoyi masu zaman na Angola suna kira ga hukumar shari'a da ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba a mayar da kadarorin tsohuwar 'yar shugaban kasa Isabel dos Santos da aka kwato daga Portugal zuwa Angola.

https://p.dw.com/p/4jnGK
Hoto: Shootpix/abaca/picture alliance

´Farkon watan Augustan wannan shekarar wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adama da kuma na yaki da cin hanci da rashawa a Angola suka shigar da kokensu zuwa ga offisoshin babban mai shari'a na kasashen Angola da kuma Portugal, inda suka nuna damuwa kan yadda har yanzu aka gaza dawowa da dukiyar 'yar tsohon shugaban kasar Isabel dos Santos da aka kwace a shekarar 2020 bayan an zarge ta da amfani da dukiyar jama'a wajen azurta kanta. 

Bildkombo Angola Ex-Vize-Präsident Manuel Domingos Vicente und Isabel dos Santos
Hoto: Li Xiaowei/Xinhua/IMAGO, Paulo Duarte/AP/picture alliance

 Wadannan manyan kungiyoyin masu zamann kansu a Angola guda hudu da ke fafatukar kare hakkin jama'a da ma yakar cin hanci da rashawa sun zargi cewa, ta yiwu Isabel dos Santos, 'yar marigayi tsohon shugaban kasar, ta karkatar da wasu makudan kudaden kasar zuwa Hadadiyar Daular Larabawa, inda nan ne take zaune ko kuma ma zuwa wasu kasashe mussaman Portugal da ta yiwa Angolan mulkin mallaka. Wadannan kungiyoyin dai sun bukaci da a gaggauta daukar mataki kan Isabel da aka zarge ta da handame kudin kasar. Guda daga cikin kakakin kungiyoyin, Maos Livres ya ce tsawon shekaru hudu kenan suna jiran tsamanin mayar da kudaden zuwa Angola domin ya amfanin 'yan kasar da dama da ke bukata. Guilherme Neves shi ne kakakin kungiyoyin:  "Abun da muke bukata ga manyan masu shari'ar a kasashen Angola da kuma Portugal shi ne su bayyana wa jama'a hakikanin abunn da yake haifar da jan kafa wajen mayar da kudaden da Isabel ta yi rif da ciki da su daga Portugal zuwa Angola."

Angola Isabel Dos Santos in Cannes
Hoto: Loic Venance/AFP

Isabel dos   Santosdai ta taba zama macen da ta fi kowace mace kudi a nahiyar Afirka, inda yawan arzikinta ya kai dala biliyan uku a wancan lokacin, sai dai kuma bincike ya nuna cewa ta azurta kanta ne ta hamramtacciyar hanya, inda ta yi kasuwanci ba bisa ka'ida da kamfanonin da ake hulda da gwamnatin mahaifinta,  José Eduardo dos Santos a wancan lokacin. Masu kwarmata bayanai na nahiyar Afirka sun bankado yadda ta yi wandaka da kudin talakawan kasar, kuma sun bai wa kungiyar kwararrun 'yan jarida masu binciken kwakwaf na kasa-da-kasa kan yadda ta gudanar da kasuwanci da kamfanoni 400 a kasashe 41 da ake ganin ta yi amfani da damar da mahaifinta ya samu na dade kan karagar mulki wajen cin karenta babu babbaka. To sai dai tun bayan bankado wannan almudahanar da aka gabatar da kwararan shaidu da za su iya tabbatar da zargin, ba a dauki wani mataki na shari'a ba. Abun da sanya, Rui Verde ke ganin cewa akwai bukatar gwamnatin Angola ta farka daga dogon barcin da take yi: " Mun ga yadda offishin babban mai shari'a na Angola ya bige da gyangyadi, A matsayinmu na masu sa ido kan bincike, har yanzu ban gano dalilin da ya sanya suke sakaci wajen gayyato Isabel ba daga Dubai. Kasar Angola na cikin hadari na rashin ganin ko fucika na kudin Isabel da aka dasa ayar tambaya a kansu."

ENDIAMA staatliches Unternehmen in Angola für Diamantengeschäfte
Hoto: Luke Dray/Getty Images

Tun bayan wancan lokaci dai Isabel ke fuskantar bincike daga hukumomin Angola kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa aka kuma rike duk wata kaddarar da take da ita a kasar, haka zalika kotuna a kasashen Birtaniya da Netherlands da Portugal sun bayar da umurnin rike kadarorinta bayan fuskantar matsin lamba daga Angola. Amma tun daga nan , ba a sake jin duriyar dukiyar da aka  kwace ba.