Takun saka tsakanin Armeniya da Azerbaijan
September 19, 2023Fiye da mutane 20 sun halaka sakamakon sabon matakin sojan da kasar Azerbaijan ta dauka na kakabe abin da ta kira 'yan ta'adda a yankin Nagorno-Karabakh da ake takaddama tsakanin kasashen Armeniya da Azerbaijan. Rasha ta ce sojojinta masu aikin tabbatar da zaman lafiya sun kwashe daruruwan fararen hula, bayan farmakin da kasar Azerbaijan ta kaddamar.
Karin Bayani: Hari bayan sulhun Armeniya da Azarbaijan
Kasar Turkiyya wadda ta goyon bayan matakin na Azerbaijan ta ce haka ya biyo bayan rashin magance damuwa da kasar ta Azerbaijan take nunawa kan abin da ke faruwa a yankin da ake takaddama. Tuni kasar Rasha ta nemi kawo karshen sabon rikicin da ya barke.
A daya hannun masu zanga-zanga a Yerevan babban birnin kasar Arminiya sun bukaci Firaminista Nikol Pashinyan ya ajiye madafun iko, bayan da ya yi ikirarin yunkurin juyin mulki bayan kasar ta Azerbaijan ta kaddamar da farmakin na wannan Talata. Daruruwan mutane suka fito zanga-zangar adawa da yadda gwamnatin ta Arminiya ta tunkari rikicin na yankin Nagorno-Karabakh da ke faruwa da kasra ta Azerbaijan.