Biden: Fata kan tsagaita wuta a Gaza
February 27, 2024Furucin na shugaba Biden na zuwa ne a daidai lokacin da dagulewar ayyukan jin kai ke neman rikidewa zuwa yunwa a zirin Gaza na yankin Falasdinu inda dakarun Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a kokarinsu na fatattakar kungiyar Hamas.
Karin bayani: Jamus ta yi kira ga Isra'ila ta kauce wa take hakkin 'dan adam a Gaza
A cewar wasu majiyoyi masu kunsanci da Hamas sabuwar yarjejeniyar za ta ba da damar tsagaita wuta na tsawon makonni shida tare da sakin ragowar mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su yayin da Isra'ila ita ma za ta sako fursunonin Falasdinawa da kuma ba da izinin shigar da kayan agaji a Gaza.
Bugu da kari wani babban jami'in Isra'ila ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Ynet cewa da akwai fatan samun nasara kan yiwuwar amincewa da sabuwar yarjejeniyar.
To sai dai a ranar Litinin sojojin Isra'ila sun gabatar wa ofishin Firaiminista Benjamin Netanyahu tsarin kwashe fararen hula daga yankunan da ake yaki domin afka wa Rafah sai dai ba a bayar da cikakken bayani kan inda za a tsugunar da su ba.