1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Burtaniya na goyon bayan Mark Rutte ya jagoranci NATO

February 22, 2024

Burtaniya ta jaddada goyon baya ga firaministan kasar Netherland Mark Rutte domin maye gurgin sakataren kawancen tsaro na NATO Jens Stoltenberg wanda ke kammala wa'adinsa a ranar daya ga watan Oktoba na 2024.

https://p.dw.com/p/4cks7
Holland Niederlande | NATO The Hague - Jens Stoltenberg und Mark Rutte
Hoto: NATO

Bayan gaza cimma matsaya kan wanda zai gaji Jens Stoltenberg a matsayin sakataren kungiyar tsaro ta NATO, Burtaniya ta fito fili ta bayyana goyon baya ga firaministan kasar Netherland Mark Rutte domin ya jarancin kawancen mai membobi 31.

Kakakin firaministan Burtaniya ya siffanta Mark Rutte mai shekaru 57 a duniya a matsayin mutum mai mutunci da kuma dattaku, sannan kuma kwararre a fannin tsaro wanda ka iya samar da muhinman tsare-tsare don kara karfin kungiyar da ke takun saka da kasar Rasha kan mamayar Ukraine.

A baya dai wasu kasashe daga cikin membin NATO sun nuna bukatar samar da mace a karon farko a matsayin jagora wa kawancen da ke cika shekaru 75 da kafuwa a wannan shekara ta 2024.

A yanzu dai kallo ya koma Amurka da za ta karbi bakuncin taron koli na kungiyar wace aka kafa a shekarar 1949 bayan yakin duniya na biyu.