1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deby na son shugabanci karo na shida

Martina Schwikowski ZU/LMJ
February 11, 2021

Duk da zanga-zangar adawa da yake fuskanta, Shugaba Idriss Déby na Chadi zai tsaya takarar shugabancin kasar a karo na shida a zaben da za a yi cikin watan Afrilun wannan shekarar.

https://p.dw.com/p/3pEWG
Tschad Präsident Idriss Deby Itno
Shugaban kasar Chadi Idris Deby ItnoHoto: Präsidentschaft von Tschad

Shugaba Idris Deby na Chadi mai shekaru 68 na son tsawaita mulkinsa har zuwa shekara ta 2033. Duk da cewa wasu daga al'ummar kasar ba sa muradin hakan, amma hukumomin Chadin sun tarwatsa zanga-zangar da 'yan adawa suka yi domin nuna turjiyarsu. Tun cikin shekarar 1990  shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno ya dare kan madafun iko. Sai dai duk da cewa ya kwashe kusan shekaru 31 yana zuba salon mulkinsa a kasar, Deby na fatan ci gaba da jagorantar Chadi a matakin wa'adi na shida idan har ya yi nasara a zaben ranar 11 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2021.

Karin Bayani: Shekaru 60 na 'yancin Chadi daga Faransa

To amma 'yan kasar masu yawa na adawa da muradin Shugaba Deby na sake tsayawa takara, inda a karshen makon da ya gabata aka yi zanga-zanga a manyan biranen Chadin ciki har da N'Djamena babban birnin kasar. Masu zanga-zanga sun kona tayoyi a kan  tituna, sai dai kuma 'yan sanda sun fesa musu barkon tsohuwa tare da kama mutane 50 daga cikin masu zanga-zangar da har yanzu ake ci gaba da tsarewa.

Tschad Succès Masra
Dan adawa a kasar Chadi Succès MasraHoto: Blaise Dariustone/DW

Fitaccen dan takarar adawa a zaben kasar Succès Masra na daya daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar, ya shaidawa DW bacin ransa: ''Muna kira ga kasashen duniya, musamman kasashen Faransa da Jamus da Amirka da su taimaka wa mutanen Chadi, ko sa sami irin 'yancin da mutane a kasashensu ke da shi. Jerin gwano na neman 'yanci muka yi a cikin ruwan sanyi ba tare da tashin hankali ba.''

Karin Bayani: 'Yan siyasar Chadi na tattauna halin da take ciki

Dan adawa Masra mai shekaru 38 dai, ba zai samu damar tsaya wa takara a zaben watan Afrilun ba kasancewar tsarin mulkin kasar ya yi tanadin sai mutum yana da shekaru 40 ne kawai zai iya tsayawa takarar shugaban kasa. Wannan ne kuma ya sa jam'iyyun adawa 16 na kasar ta Chadi suka kulla kawance tare da tsayar da Théophile Bongoro domin su goya masa baya ya samu karfin da zai iya kwace goruba a hannun Shugaba Idris Deby. Ko da yake Roland Marchal wani mai sharhi a kasar na shakkun ko wannan kawancen zai iya kai labari. Shugaba Idris Deby na kasar ta Chadi dai na da tarihin amfani da dabaru kala-kala wujen rufe bakunan 'yan hamayya. Cikin abubuwan da shugaban ya yi kaurin suna da su har da haramta zanga-zanga ko kuma toshe shafukan sada zumunta. Ga misali, an rufe shiga kafar intanet na watanni 10 a lokacin da gwamnatin kasar ta kwaskware kundin tsarin mulki a shekara ta 2018.