Chadi ta waiwayi wadanda Hissene Habre ya azabtar
March 6, 2024Wata kungiya mai zaman kanta ce ta sanar da hakan inda ta ce kudin da za a ba wa mutanen ya kai akalla dala milyan 16 da dubu 500.
Habre da ake yiwa lakabi da ''Pinochet na Afrika", ya fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai 2017 a kotun hukunta laifukan yaki ta musamman sakamakon rawar da ya taka wajen keta hakkin 'dan adam, da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 40 a lokacin mulkinsa a Chadi.
Karin bayani:An sallami Hissene Habre daga kurkuku
Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam na kasar ta Chadi Djidda Oumar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa akwai mutanen da lamarin ya shafa kimanin 10,800 da kowannensu zai samu CFA 925,000 kwatankwacin dalar Amurka $1,529.
Karin bayani: Chadi: Wadanda aka azabtar sun koka da rashin diyya
Hissene Habre ya mulki kasar ta Chadi tun daga 1982 har zuwa lokacin da Marigayi Idris Deby Itno ya hambarar da gwamnatinsa a 1990, inda zakara ya ba shi sa a ya tsallaka kasar waje.