1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madrid: Taron COP25 kan yanayi

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 12, 2019

Al'ummomin kasa da kasa sun hadu a birnin Madrid na kasar Spain, da nufin lalubo mafita kan sauyi ko kuma dumamar yanayi da ke kara ta'azzara a duniya.

https://p.dw.com/p/3UiIX
Spanien Madrid l  25. UN-Klimakonferenz - Logo
Hoto: Getty Images/P. Blazquez Dominguez

Taron Madrid na bana zai yi kokarin zakulo hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar dumamam ko kuma sauyin yanayi da ke zaman barazana ga dorewar duniyar. Rahotanni sun nunar da cewa shekarun 2010 zuwa 2019 sun kasance shekarun da suka fi tsananin zafi a tarihin duniya. Kiyasi dai ya nunar da cewa abin ya karu domin kuwa 2019 ta fi ko wacce shekara zafi a tarihin.