1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen babbar Sallah a Najeriya da Nijar

Nasir Salisu Zango LMH
July 19, 2021

A daidai lokacin da ake shirin hawan idin babbar Sallah, a Najeriya hukumomi a Kano sun dakatar da hawan Sallah bisa fargabar corona, a yayin da Jamhuriyar Nijar farashin dabbobi ya zarta masu karamin karfi a bana.

https://p.dw.com/p/3whvt
 Burkina Faso | Schafe
Hoto: Richard Tiéné/DW

Da farin matsalar rashin kudi da hauhawar kayan masarufi su suka so dakushe tasirin hawan sallar na bana a Najeriya, ko da yake sanarwar da mahukuntan kasar suka bayar na dage yin hawan sallah wasu yankunan ciki har da Kano sun dagula al'amurra a zukatan jama'a masu zumudin ganin ranar sallah ta zo. Hukumomi a Najeriya na hasashen hawan sallar ka iya kara yaduwar annobar cutar corona samfarin Delta mai saukin yaduwa, lamarin da ya sa mahukuntan Kano suka soke hawan salla da hawan dawaki da sarkin Kano da hakaimmai ke yi a kowace shekara.

Wannan matakin ya kara gishiri a gyambon rashin armashin bukukuwan Sallah bana a Jihar Kano. wanda ya sa da dama cewar abin yayi yawa ga mari ga kuma tsinka jaka. Sai dai wasu da suka zanta da DW sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta na ganin muhimmancin matakin da masu ganin akasin haka, a yayin da a bangarensu malamai ke cewa da a yiwa matakin da hukumomin suka dauka mai nasaba da kiwon lafiyar al'umma biyayya sau da kafa.

Karikatur: Takunkumi
Hoto: DW

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatan jihar Kano da dama ba su samu albashinsu ba bayan sun sa ran cewa gwamnatin jihar za ta yi albashin a cikin lokaci don tallafa masu yin sallar a cikin farin ciki.

Karin Bayani: Idin Babbar Salla a lokacin coronavirus

Sabanin Jihar Kano a Damagaram a Jamhuriyar Nijar komai na tafiya a cikin tsanaki, duk da yake hukumomi ba su dakatar da hawan Sallah ba, ko kuma daukar wasu matakai na takaita haduwar jama'a, farashin dabbobi ya yi tashin gwabron zabo a yankin sa'o'i kafin hawan Sallah. A kasuwannin birni da karkara farashin raguna ya tashi, inda wasu ke cewa rabon da su da hakan an jima, kamar yadda wakilin DW Hausa ya tarar ana cinikin raguna inda farashin ya bambanta daga wani ragon zuwa wani.

A wannan karon ba kamar yadda aka saba gani ba, inda a kananan hukumomi kungiyoyi masu zaman kansu a Damagaram sukan bude baje kolin ragunan Layya dan sayarwa da farashi mai rahusa, a bana hakan bai samu ba a yankuna da dama na Damagaram, sai dai kuma farashin kayan yajin da ke taka rawa wajen kara inganta bukukuwan Layyar ya dan zarta fiye da na bara.