Najeriya ta samar da allurar corona
March 23, 2021A baya dai Tarayyar Najeriyar na zaman guda cikin kasashen da ke fadin Allah baku mu samu, dangane da batun riga-kafin annobar ta COVID-19. Kuma tuni kasar ta karbi allurar AstraZeneca ta kasar Ingila, da yawanta ya doshi miliyan hudu. To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce jami'an kimiyarta sun gano akalla allurai guda biyu da ke jiran gwaji da amincewa, a kan hanyar tunkarar annobar da ke tashi da lafawa a duniya a halin yanzu.
Karin Bayani: Rudani kan samar da riga-kafin coronavirus a Najeriya
Masana a jami'ar Redeem da ke garin Ede cikin jihar Osun ne dai suka bayyana gano allurar da a cewarsu, ke nuna alamun nasarar da ta kai kaso 90 cikin 100 a yakin annobar ta COVID-19. To sai dai kuma ma'aikatar lafiyar kasar ta bakin Dakta Ibrahim Kana da ke zaman darakta a Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa, cibiyar na bukatar kimanin dalar Amirka miliyan 100 kafin kai wa ga tabbatar da gwajin allurar.
Ko ya zuwa ina ake shirin zuwa da nufin samar da kudin gwajin allurar riga-kafin dai, sannu a hankali Najeriyar na dada nisa a cikin yi wa al'ummarta riga-kafin 'yar kyauta. Duk da cewar dai kasar ta karbi abun da ya kai kusan allurar miliyan hudu. Da kyar da gumin goshi ne dai aka samu yi wa mutane dubu 150, a cikin tsawon kusan makonni uku. Ya zuwa yanzu dai babu abun da ke gudana a jihohi kusan guda takwas, saboda karuwar adawar da al'ummarsu ke yi da allurar ta COVID-19.
Karin Bayani: Matakan riga-kafin cutar corona a Najeiya
To sai dai kuma a fadar Dakta Ado Mohammed da ke zaman tsohon shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta kasar, adawa da riga-kafin annoba a cikin Najeriya bai zama sabo ba. Ko bayan jankafa cikin allurar mai tasiri dai, wata matsalar da ke zaman ruwan dare a cikin riga-kafin allurar na zaman cuwa-cuwa da ke dada bazuwa a cibiyoyin allurar dabam-dabam. Abun kuma da a cewar ma'aikata ta lafiyar Najeriyar ke zaman matsala babba. Duk da cewar dai yawan annobar coronan na dada raguwa, akwai tsoron samun cikas ga allurar na iya mai da hannun agogo zuwa baya, a kokari na yakar annobar da ke tashi da lafa wa a duniya baki daya.