1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mokamar fannin illimi sanadiyyar Covid-19

July 13, 2020

Kungiyar agaji ta Save the Children ta fitar da gargadin cewa akwai yara kimanin miliyan 10 da ba za su samu komawa makaranta ba bayan samun saukin cutar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3fGdq
Nigeria Abuja 2014 | Studenten & Ergebnis der Prüfungen
Hoto: Imago Images/Xinhua Afrika

Cutar COVID-19 dai ta tilasta rufe makarantu ba kawai a Najeriya ba har ma da sauran sassan duniya, abin da ya haifar da koma baya a kokarin ilmantar da al'umma manya da yara. Wannan ya sa kungiyar agaji ta Save the Children ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa za a samu akalla yara sama da miliyan 10 da za su fice a makaranta saboda wannan mataki na rufe makarantun domin yaki da cutar COVID-19. Wannan rahoto ya tada hankulan masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi musamman ganin a sashen Arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin areacin kasar ana ma kokarin fahimtar da jama'a muhimmancin ilimin ne kansa sai kuma ga matsalar dakatar da karatun.


Malam Sale Shu'aibu Al-Gidimy wani masanin ilimi ne na zamani da na addini wanda ya kwashe tsawon rayuwarsa yana koyarwa a makarantun Firarmare da Sakandare a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

"Wannan zama da ake yi da ba a san ranar karewarsa ba, tabbas zai sa yara da yawa ba su koma makaranta ba don iyaye za su tura yaransu sana'o'i. Da can ma da suke zuwa makarantar iyaye kan damu da 'yan kwanakin da ba a karatu ka ga suna wasan kallon kafa a unguwanni su dami iyaye da sauran mutane."

Illimin yara mata ya fi fuskantar matsala a akasarin kasashen Afrika
Illimin yara mata ya fi fuskantar matsala a akasarin kasashen AfrikaHoto: AFP/N. Delaunay

Yanzu haka masana sun bayyana cewa an samu karuwar yara da ke gararamba a kan hanyoyi saboda kasancewa makarantu a rufe duk da cewa akwai iyaye da ke nuna damuwa a kan rashin zuwan 'ya'yansu makaranta yayin da ga wasu akasin hakan ne.
 

Dalibai ma da wannan rufe makarantu ya shafa na nuna damuwa musamman ganin yawancin abokan karatunsu an cire su a makaranta kamar yadda Usman Mustapha wani dalibi ya bayyana.
 

Su kuma kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkin mata na cewa babu wanda wannan matsala ta fi shafa kamar mata domin kuwa ilimin mata ne ke kara samun koma baya.

Sai dai duk kokarin da wakilinmu Al'amin  Sulaiman Muhammad ya yi domin jin ta bakin hukumomi don sanin matakan da suke dauka ya ci tura.
 

Sai dai masharhanta na ba da shawara hukumomi su fito da hanyoyi na koyar da yara ko da a gida ne watakila a samu saukin cire yara a makarantu musamman a wannan sashe da ake ganin akwai kungiyoyin da ke yaki da irin wannan tsari na karatu da burinsu zai cika in aka ci gaba da cire yara a makarantu.