Za a magance matsalar tsaro a Najeriya
August 23, 2023Kwanaki da kaiwa ya zuwa ga rantsar da sabuwar majalisar ministocin Tarrayar Najeriya, sabbabin 'yan mulkin tarrayar Najeriya sun ce suna bukatar kai karshen annobar rashin tsaron kasar cikin tsawon shekara daya tal. Sabo na ministan tsaron kasar Badaru Abubakar dai ya nemi manyan hafsoshi na tsaron kasar da su bai wa gwamnatin bukatu na kudi da kila kayan aiki kan hanyar iya kai wa ga fidda A'in da ke cikin rama a halin yanzu. Badarun da ya gana da jami'an tsaron kasar bayan kamun aiki dai ya ce shugaban kasar na shirye ya bai wa jami'an tsaro daukaci na bukatu da nufin kaiwa ga bukatar da ke zaman mai girma. Daga yanzun nan zan nemi manyan hafsoshi na tsaro da su bani bukatu da kuma lokaci da ma tsarin kaiwa ya zuwa warware matsalolin daya bayan daya. Shugaba Buhari dai alal ga misali ya karya kumallo tare da wa'adin wattani guda sbhida, amma kuma ya kashe tsabar kudi kusan triliyan na Naira ta kasar dai-dai har 10 cikin batun rashin tsaron kafin kare mulkin na shekaru Takwas. Tsohuwa ta gwamnatin da ta shude dai ta rika kallon takara tsakanin sojojin ko bayan gaza hada kai da ragowa na jami'an tsaron cikin batun rashin tsaron,da ya koma kafa ta tara na goro maimakon kokari na ceton al'umma Najeriya ga kokarin kasar na farfadowa da kila ma gwada tasirin ta na mafi girma ga tattali na arziki a nahiyar Afirka.